The Quran in Hausa - Surah Fatiha translated into Hausa, Surah Al-Fatihah in Hausa. We provide accurate translation of Surah Fatiha in Hausa - الهوسا, Verses 7 - Surah Number 1 - Page 1.
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ (1) Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai |
الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (2) Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu |
الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ (3) Mai rahama, Mai jin ƙai |
مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ (4) Mai nuna Mulkin Rãnar Sakamako |
إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ (5) Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa |
اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ (6) Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya |
صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ (7) Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba |