The Quran in Hausa - Surah Qariah translated into Hausa, Surah Al-Qariah in Hausa. We provide accurate translation of Surah Qariah in Hausa - الهوسا, Verses 11 - Surah Number 101 - Page 600.
الْقَارِعَةُ (1) Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro) |
مَا الْقَارِعَةُ (2) Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْقَارِعَةُ (3) Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa |
يَوْمَ يَكُونُ النَّاسُ كَالْفَرَاشِ الْمَبْثُوثِ (4) Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa |
وَتَكُونُ الْجِبَالُ كَالْعِهْنِ الْمَنفُوشِ (5) Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe |
فَأَمَّا مَن ثَقُلَتْ مَوَازِينُهُ (6) To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi |
فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ (7) To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda |
وَأَمَّا مَنْ خَفَّتْ مَوَازِينُهُ (8) Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi) |
فَأُمُّهُ هَاوِيَةٌ (9) To, uwarsa Hãwiya ce |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا هِيَهْ (10) Kuma me ya sanar da kai mece ce ita |
نَارٌ حَامِيَةٌ (11) Wata wuta ce mai kuna |