The Quran in Hausa - Surah Adiyat translated into Hausa, Surah Al-Adiyat in Hausa. We provide accurate translation of Surah Adiyat in Hausa - الهوسا, Verses 11 - Surah Number 100 - Page 599.
وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا (1) Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki |
فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا (2) Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa |
فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا (3) Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba |
فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا (4) Sai su motsar da ƙũra game da shi |
فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا (5) Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya |
إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ (6) Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa |
وَإِنَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ (7) Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka |
وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ (8) Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne |
۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ (9) Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura |
وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ (10) Aka bayyana abin da ke cikin zukata |
إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌ (11) Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne |