The Quran in Hausa - Surah Duha translated into Hausa, Surah Ad-Dhuha in Hausa. We provide accurate translation of Surah Duha in Hausa - الهوسا, Verses 11 - Surah Number 93 - Page 596.
وَالضُّحَىٰ (1) Inã rantsuwa da hantsi |
وَاللَّيْلِ إِذَا سَجَىٰ (2) Da dare a lõkacin da ya rufe (da duhunsa) |
مَا وَدَّعَكَ رَبُّكَ وَمَا قَلَىٰ (3) Ubangijinka bai yi maka bankwana ba, kuma bai ƙĩ kaba |
وَلَلْآخِرَةُ خَيْرٌ لَّكَ مِنَ الْأُولَىٰ (4) Kuma lalle ta ƙarshe* ce mafi alheri a gare ka daga ta farko |
وَلَسَوْفَ يُعْطِيكَ رَبُّكَ فَتَرْضَىٰ (5) Kuma lalle ne, Ubangijinka zai yi ta bã ka kyauta sai ka yarda |
أَلَمْ يَجِدْكَ يَتِيمًا فَآوَىٰ (6) Ashe, bai sãme ka marãya ba, sa'an nan Ya yi maka makõma |
وَوَجَدَكَ ضَالًّا فَهَدَىٰ (7) Kuma Ya sãme ka bã ka da shari'ã, sai Ya shiryar da kai |
وَوَجَدَكَ عَائِلًا فَأَغْنَىٰ (8) Kuma Ya sãme ka matalauci, sai Ya wadãtã ka |
فَأَمَّا الْيَتِيمَ فَلَا تَقْهَرْ (9) Sabõda haka, amma marãya, to, kada ka rinjãye shi |
وَأَمَّا السَّائِلَ فَلَا تَنْهَرْ (10) Kuma amma mai tambaya, kada ka yi masa tsãwa |
وَأَمَّا بِنِعْمَةِ رَبِّكَ فَحَدِّثْ (11) Kuma amma ni'imar Ubangijinka, sai ka faɗa (dõmin gõdiya) |