The Quran in Hausa - Surah Sharh translated into Hausa, Surah Ash-Sharh in Hausa. We provide accurate translation of Surah Sharh in Hausa - الهوسا, Verses 8 - Surah Number 94 - Page 596.
أَلَمْ نَشْرَحْ لَكَ صَدْرَكَ (1) Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta) |
وَوَضَعْنَا عَنكَ وِزْرَكَ (2) Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe |
الَّذِي أَنقَضَ ظَهْرَكَ (3) Wanda ya nauyayi bãyanka |
وَرَفَعْنَا لَكَ ذِكْرَكَ (4) Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka |
فَإِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (5) To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi |
إِنَّ مَعَ الْعُسْرِ يُسْرًا (6) Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi |
فَإِذَا فَرَغْتَ فَانصَبْ (7) Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah) |
وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَارْغَب (8) Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi |