The Quran in Hausa - Surah Humazah translated into Hausa, Surah Al-Humazah in Hausa. We provide accurate translation of Surah Humazah in Hausa - الهوسا, Verses 9 - Surah Number 104 - Page 601.

| وَيْلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ (1) Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa)  | 
| الَّذِي جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُ (2) Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa  | 
| يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُ أَخْلَدَهُ (3) Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi  | 
| كَلَّا ۖ لَيُنبَذَنَّ فِي الْحُطَمَةِ (4) A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama  | 
| وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحُطَمَةُ (5) Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama  | 
| نَارُ اللَّهِ الْمُوقَدَةُ (6) Wutar Allah ce wadda ake hurawa  | 
| الَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى الْأَفْئِدَةِ (7) Wadda take lẽƙãwa a kan zukata  | 
| إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌ (8) Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu  | 
| فِي عَمَدٍ مُّمَدَّدَةٍ (9) A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu  |