القرآن باللغة الهوسا - سورة الهُمَزَة مترجمة إلى اللغة الهوسا، Surah Humazah in Hausa. نوفر ترجمة دقيقة سورة الهُمَزَة باللغة الهوسا - Hausa, الآيات 9 - رقم السورة 104 - الصفحة 601.

| وَيْلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ (1) Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) |
| الَّذِي جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُ (2) Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa |
| يَحْسَبُ أَنَّ مَالَهُ أَخْلَدَهُ (3) Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi |
| كَلَّا ۖ لَيُنبَذَنَّ فِي الْحُطَمَةِ (4) A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama |
| وَمَا أَدْرَاكَ مَا الْحُطَمَةُ (5) Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama |
| نَارُ اللَّهِ الْمُوقَدَةُ (6) Wutar Allah ce wadda ake hurawa |
| الَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى الْأَفْئِدَةِ (7) Wadda take lẽƙãwa a kan zukata |
| إِنَّهَا عَلَيْهِم مُّؤْصَدَةٌ (8) Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu |
| فِي عَمَدٍ مُّمَدَّدَةٍ (9) A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu |