The Quran in Hausa - Surah Al Fil translated into Hausa, Surah Al-Fil in Hausa. We provide accurate translation of Surah Al Fil in Hausa - الهوسا, Verses 5 - Surah Number 105 - Page 601.
أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِأَصْحَابِ الْفِيلِ (1) Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa* ba |
أَلَمْ يَجْعَلْ كَيْدَهُمْ فِي تَضْلِيلٍ (2) Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba |
وَأَرْسَلَ عَلَيْهِمْ طَيْرًا أَبَابِيلَ (3) Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsãye, jama'a-jama'a |
تَرْمِيهِم بِحِجَارَةٍ مِّن سِجِّيلٍ (4) Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta |
فَجَعَلَهُمْ كَعَصْفٍ مَّأْكُولٍ (5) Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye |