القرآن باللغة الهوسا - سورة العاديات مترجمة إلى اللغة الهوسا، Surah Adiyat in Hausa. نوفر ترجمة دقيقة سورة العاديات باللغة الهوسا - Hausa, الآيات 11 - رقم السورة 100 - الصفحة 599.

| وَالْعَادِيَاتِ ضَبْحًا (1) Ina rantsuwa da dawãki mãsu gudu suna fitar da kũkan ciki |
| فَالْمُورِيَاتِ قَدْحًا (2) Mãsu ƙyasta wuta (da kõfatansu a kan duwatsu) ƙyastawa |
| فَالْمُغِيرَاتِ صُبْحًا (3) Sa'an nan mãsu yin hari a lokacin asuba |
| فَأَثَرْنَ بِهِ نَقْعًا (4) Sai su motsar da ƙũra game da shi |
| فَوَسَطْنَ بِهِ جَمْعًا (5) Sai su shiga, game da ita (ƙũrar), a tsakãnin jama'ar maƙiya |
| إِنَّ الْإِنسَانَ لِرَبِّهِ لَكَنُودٌ (6) Lalle ne mutum mai tsananin butulci ne ga Ubangijinsa |
| وَإِنَّهُ عَلَىٰ ذَٰلِكَ لَشَهِيدٌ (7) Lalle ne shi mai shaida ne a kan laifinsa da haka |
| وَإِنَّهُ لِحُبِّ الْخَيْرِ لَشَدِيدٌ (8) Kuma alle ne ga dũkiya shi mai tsananin so ne |
| ۞ أَفَلَا يَعْلَمُ إِذَا بُعْثِرَ مَا فِي الْقُبُورِ (9) Shin, bã ya da sanin lõkacin da aka tõne abin da yake cikin kaburbura |
| وَحُصِّلَ مَا فِي الصُّدُورِ (10) Aka bayyana abin da ke cikin zukata |
| إِنَّ رَبَّهُم بِهِمْ يَوْمَئِذٍ لَّخَبِيرٌ (11) Lalle ne Ubangijinsu, game da su a ranar nan Mai ƙididdigewa ne |