وَالسَّمَاءِ وَالطَّارِقِ (1) Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare |
وَمَا أَدْرَاكَ مَا الطَّارِقُ (2) To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare |
النَّجْمُ الثَّاقِبُ (3) Shi ne taurãron nan mai tsananin haske |
إِن كُلُّ نَفْسٍ لَّمَّا عَلَيْهَا حَافِظٌ (4) Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro |
فَلْيَنظُرِ الْإِنسَانُ مِمَّ خُلِقَ (5) To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi |
خُلِقَ مِن مَّاءٍ دَافِقٍ (6) An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna |
يَخْرُجُ مِن بَيْنِ الصُّلْبِ وَالتَّرَائِبِ (7) Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji |
إِنَّهُ عَلَىٰ رَجْعِهِ لَقَادِرٌ (8) Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne |
يَوْمَ تُبْلَى السَّرَائِرُ (9) Rãnar da ake jarrabawar asirai |
فَمَا لَهُ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ (10) Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah) |
وَالسَّمَاءِ ذَاتِ الرَّجْعِ (11) Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa |
وَالْأَرْضِ ذَاتِ الصَّدْعِ (12) Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa |
إِنَّهُ لَقَوْلٌ فَصْلٌ (13) Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki |
وَمَا هُوَ بِالْهَزْلِ (14) Kuma shĩ bã bananci* bane |
إِنَّهُمْ يَكِيدُونَ كَيْدًا (15) Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai |
وَأَكِيدُ كَيْدًا (16) Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi |
فَمَهِّلِ الْكَافِرِينَ أَمْهِلْهُمْ رُوَيْدًا (17) Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu |