Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 102 - البَقَرَة - Page - Juz 1
﴿وَٱتَّبَعُواْ مَا تَتۡلُواْ ٱلشَّيَٰطِينُ عَلَىٰ مُلۡكِ سُلَيۡمَٰنَۖ وَمَا كَفَرَ سُلَيۡمَٰنُ وَلَٰكِنَّ ٱلشَّيَٰطِينَ كَفَرُواْ يُعَلِّمُونَ ٱلنَّاسَ ٱلسِّحۡرَ وَمَآ أُنزِلَ عَلَى ٱلۡمَلَكَيۡنِ بِبَابِلَ هَٰرُوتَ وَمَٰرُوتَۚ وَمَا يُعَلِّمَانِ مِنۡ أَحَدٍ حَتَّىٰ يَقُولَآ إِنَّمَا نَحۡنُ فِتۡنَةٞ فَلَا تَكۡفُرۡۖ فَيَتَعَلَّمُونَ مِنۡهُمَا مَا يُفَرِّقُونَ بِهِۦ بَيۡنَ ٱلۡمَرۡءِ وَزَوۡجِهِۦۚ وَمَا هُم بِضَآرِّينَ بِهِۦ مِنۡ أَحَدٍ إِلَّا بِإِذۡنِ ٱللَّهِۚ وَيَتَعَلَّمُونَ مَا يَضُرُّهُمۡ وَلَا يَنفَعُهُمۡۚ وَلَقَدۡ عَلِمُواْ لَمَنِ ٱشۡتَرَىٰهُ مَا لَهُۥ فِي ٱلۡأٓخِرَةِ مِنۡ خَلَٰقٖۚ وَلَبِئۡسَ مَا شَرَوۡاْ بِهِۦٓ أَنفُسَهُمۡۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ﴾
[البَقَرَة: 102]
﴿واتبعوا ما تتلوا الشياطين على ملك سليمان وما كفر سليمان ولكن الشياطين﴾ [البَقَرَة: 102]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma suka bi abin da shaiɗanu* ke karantawa a kan mulkin Sulaimanu, kuma Sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma Shaidanun, su ne suka yi kafirci, suna karantar da mutane sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan mala'iku biyu a Babila, Haruta da Maruta. Kuma ba su sanar da kowa ba balle su ce: "Mu fitina kawai ne, saboda haka kada ka kafirta," balle har su yi ta neman ilmin abin da suke rarrabewa tsakanin mutum da matarsa da shi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) ba su zama masu cutar da kowa da shi ba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilmin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, ba ya da wani rabo a cikin Lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi, da sun kasance suna sani |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma suka bi abin da shaiɗanu ke karantawa a kan mulkin Sulaimanu, kuma Sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma Shaidanun, su ne suka yi kafirci, suna karantar da mutane sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan mala'iku biyu a Babila, Haruta da Maruta. Kuma ba su sanar da kowa ba balle su ce: "Mu fitina kawai ne, saboda haka kada ka kafirta," balle har su yi ta neman ilmin abin da suke rarrabewa tsakanin mutum da matarsa da shi daga gare su. Kuma su (masu yin sihirin) ba su zama masu cutar da kowa da shi ba, face da iznin Allah. Kuma suna neman ilmin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, ba ya da wani rabo a cikin Lahira. Kuma tir da abin da suka sayar da rayukansu da shi, da sun kasance suna sani |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma suka bi abin da shaiɗãnu ke karantawa a kan mulkin Sulaimãnu, kuma Sulaimãnu bai yi kãfirci ba, kuma Shaidãnun, sũ ne suka yi kãfirci, suna karantar da mutãne sihiri. Kuma ba a saukar da shi ba a kan malã'iku biyu a Bãbila, Harũta da Mãrũta. Kuma ba su sanar da kõwa ba balle su ce: "Mũ fitina kawai ne, sabõda haka kada ka kãfirta," balle har su yi ta nẽman ilmin abin da suke rarrabẽwa tsakãnin mutum da mãtarsa da shi daga gare su. Kuma su (mãsu yin sihirin) ba su zama mãsu cũtar da kõwa da shi ba, fãce da iznin Allah. Kuma suna nẽman ilmin abin da yake cũtar da su, kuma bã ya amfaninsu. Kuma lalle ne, haƙiƙa, sun sani, tabbas, wanda ya saye shi, bã ya da wani rabo a cikin Lãhira. Kuma tir da abin da suka sayar da rãyukansu da shi, dã sun kasance suna sani |