وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا (1) Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi |
وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا (2) Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi |
وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا (3) Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo |
فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا (4) Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre |
فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا (5) Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni |
يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ (6) Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa |
تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ (7) Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye |
قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ (8) Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne |
أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ (9) Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu |
يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ (10) Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu |
أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً (11) Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu |
قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ (12) Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya |
فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ (13) To, ita kam, tsãwa guda kawai ce |
فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ (14) Sai kawai gã su a bãyan ƙasa |
هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ (15) Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka |
إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى (16) A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã |
اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ (17) Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi |
فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰ أَن تَزَكَّىٰ (18) Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka |
وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ (19) Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa |
فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَىٰ (20) Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma |
فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ (21) Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni) |
ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ (22) Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri |
فَحَشَرَ فَنَادَىٰ (23) Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira |
فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَىٰ (24) Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka |
فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَىٰ (25) Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko |
إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ (26) Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah |
أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَا (27) Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta |
رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا (28) Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta |
وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا (29) Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta |
وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا (30) Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta |
أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا (31) Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta |
وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا (32) Da duwatsu, Yã kafe ta |
مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ (33) Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku |
فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ (34) To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo |
يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَىٰ (35) Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata |
وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ (36) Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani |
فَأَمَّا مَن طَغَىٰ (37) To, amma wanda ya yi girman kai |
وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (38) Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya) |
فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَىٰ (39) To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma |
وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَىٰ (40) Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai |
فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَىٰ (41) To, lalle ne Aljanna ita ce makõma |
يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا (42) Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta |
فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا (43) Me ya haɗã ka da ambatonta |
إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَاهَا (44) Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake |
إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا (45) Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta |
كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا (46) Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa |