| وَالنَّازِعَاتِ غَرْقًا (1) Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi
 | 
| وَالنَّاشِطَاتِ نَشْطًا (2) Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi
 | 
| وَالسَّابِحَاتِ سَبْحًا (3) Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo
 | 
| فَالسَّابِقَاتِ سَبْقًا (4) Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre
 | 
| فَالْمُدَبِّرَاتِ أَمْرًا (5) Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni
 | 
| يَوْمَ تَرْجُفُ الرَّاجِفَةُ (6) Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa
 | 
| تَتْبَعُهَا الرَّادِفَةُ (7) Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye
 | 
| قُلُوبٌ يَوْمَئِذٍ وَاجِفَةٌ (8) Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne
 | 
| أَبْصَارُهَا خَاشِعَةٌ (9) Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu
 | 
| يَقُولُونَ أَإِنَّا لَمَرْدُودُونَ فِي الْحَافِرَةِ (10) Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu
 | 
| أَإِذَا كُنَّا عِظَامًا نَّخِرَةً (11) Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu
 | 
| قَالُوا تِلْكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ (12) Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya
 | 
| فَإِنَّمَا هِيَ زَجْرَةٌ وَاحِدَةٌ (13) To, ita kam, tsãwa guda kawai ce
 | 
| فَإِذَا هُم بِالسَّاهِرَةِ (14) Sai kawai gã su a bãyan ƙasa
 | 
| هَلْ أَتَاكَ حَدِيثُ مُوسَىٰ (15) Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka
 | 
| إِذْ نَادَاهُ رَبُّهُ بِالْوَادِ الْمُقَدَّسِ طُوًى (16) A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã
 | 
| اذْهَبْ إِلَىٰ فِرْعَوْنَ إِنَّهُ طَغَىٰ (17) Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi
 | 
| فَقُلْ هَل لَّكَ إِلَىٰ أَن تَزَكَّىٰ (18) Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka
 | 
| وَأَهْدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخْشَىٰ (19) Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa
 | 
| فَأَرَاهُ الْآيَةَ الْكُبْرَىٰ (20) Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma
 | 
| فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ (21) Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni)
 | 
| ثُمَّ أَدْبَرَ يَسْعَىٰ (22) Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri
 | 
| فَحَشَرَ فَنَادَىٰ (23) Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira
 | 
| فَقَالَ أَنَا رَبُّكُمُ الْأَعْلَىٰ (24) Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka
 | 
| فَأَخَذَهُ اللَّهُ نَكَالَ الْآخِرَةِ وَالْأُولَىٰ (25) Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko
 | 
| إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبْرَةً لِّمَن يَخْشَىٰ (26) Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah
 | 
| أَأَنتُمْ أَشَدُّ خَلْقًا أَمِ السَّمَاءُ ۚ بَنَاهَا (27) Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta
 | 
| رَفَعَ سَمْكَهَا فَسَوَّاهَا (28) Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta
 | 
| وَأَغْطَشَ لَيْلَهَا وَأَخْرَجَ ضُحَاهَا (29) Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta
 | 
| وَالْأَرْضَ بَعْدَ ذَٰلِكَ دَحَاهَا (30) Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta
 | 
| أَخْرَجَ مِنْهَا مَاءَهَا وَمَرْعَاهَا (31) Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta
 | 
| وَالْجِبَالَ أَرْسَاهَا (32) Da duwatsu, Yã kafe ta
 | 
| مَتَاعًا لَّكُمْ وَلِأَنْعَامِكُمْ (33) Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku
 | 
| فَإِذَا جَاءَتِ الطَّامَّةُ الْكُبْرَىٰ (34) To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo
 | 
| يَوْمَ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ مَا سَعَىٰ (35) Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata
 | 
| وَبُرِّزَتِ الْجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ (36) Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani
 | 
| فَأَمَّا مَن طَغَىٰ (37) To, amma wanda ya yi girman kai
 | 
| وَآثَرَ الْحَيَاةَ الدُّنْيَا (38) Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya)
 | 
| فَإِنَّ الْجَحِيمَ هِيَ الْمَأْوَىٰ (39) To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma
 | 
| وَأَمَّا مَنْ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِ وَنَهَى النَّفْسَ عَنِ الْهَوَىٰ (40) Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai
 | 
| فَإِنَّ الْجَنَّةَ هِيَ الْمَأْوَىٰ (41) To, lalle ne Aljanna ita ce makõma
 | 
| يَسْأَلُونَكَ عَنِ السَّاعَةِ أَيَّانَ مُرْسَاهَا (42) Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta
 | 
| فِيمَ أَنتَ مِن ذِكْرَاهَا (43) Me ya haɗã ka da ambatonta
 | 
| إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَاهَا (44) Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake
 | 
| إِنَّمَا أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخْشَاهَا (45) Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta
 | 
| كَأَنَّهُمْ يَوْمَ يَرَوْنَهَا لَمْ يَلْبَثُوا إِلَّا عَشِيَّةً أَوْ ضُحَاهَا (46) Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa
 |