Quran with Hausa translation - Surah Yunus ayat 24 - يُونس - Page - Juz 11
﴿إِنَّمَا مَثَلُ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا كَمَآءٍ أَنزَلۡنَٰهُ مِنَ ٱلسَّمَآءِ فَٱخۡتَلَطَ بِهِۦ نَبَاتُ ٱلۡأَرۡضِ مِمَّا يَأۡكُلُ ٱلنَّاسُ وَٱلۡأَنۡعَٰمُ حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذَتِ ٱلۡأَرۡضُ زُخۡرُفَهَا وَٱزَّيَّنَتۡ وَظَنَّ أَهۡلُهَآ أَنَّهُمۡ قَٰدِرُونَ عَلَيۡهَآ أَتَىٰهَآ أَمۡرُنَا لَيۡلًا أَوۡ نَهَارٗا فَجَعَلۡنَٰهَا حَصِيدٗا كَأَن لَّمۡ تَغۡنَ بِٱلۡأَمۡسِۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ ٱلۡأٓيَٰتِ لِقَوۡمٖ يَتَفَكَّرُونَ ﴾
[يُونس: 24]
﴿إنما مثل الحياة الدنيا كماء أنـزلناه من السماء فاختلط به نبات الأرض﴾ [يُونس: 24]
Abubakar Mahmood Jummi Abin sani kawai, misalin rayuwar duniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutane da dabbobi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinariyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutanenta suka zaci cewa su ne masu ikon yi a kanta, sai umurnin Mu ya je mata da dare ko kuma da rana, sai Mu maisheta girbabba kamar ba ta wadata ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ayoyi, daki-daki, ga mutane waɗan da suke tunani |
Abubakar Mahmoud Gumi Abin sani kawai, misalin rayuwar duniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutane da dabbobi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinariyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutanenta suka zaci cewa su ne masu ikon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare ko kuma da rana, sai Mu maisheta girbabba kamar ba ta wadata ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ayoyi, daki-daki, ga mutane waɗanda suke tunani |
Abubakar Mahmoud Gumi Abin sani kawai, misãlin rãyuwar dũniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutãne da dabbõbi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinãriyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutãnenta suka zaci cẽwa sũ ne mãsu ĩkon yi a kanta, sai umurninMu ya je mata da dare kõ kuma da rãna, sai Mu maishẽta girbabba kamar ba ta wadãta ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ãyõyi, daki-daki, ga mutãne waɗanda suke tunãni |