Quran with Hausa translation - Surah Al-Kahf ayat 19 - الكَهف - Page - Juz 15
﴿وَكَذَٰلِكَ بَعَثۡنَٰهُمۡ لِيَتَسَآءَلُواْ بَيۡنَهُمۡۚ قَالَ قَآئِلٞ مِّنۡهُمۡ كَمۡ لَبِثۡتُمۡۖ قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٖۚ قَالُواْ رَبُّكُمۡ أَعۡلَمُ بِمَا لَبِثۡتُمۡ فَٱبۡعَثُوٓاْ أَحَدَكُم بِوَرِقِكُمۡ هَٰذِهِۦٓ إِلَى ٱلۡمَدِينَةِ فَلۡيَنظُرۡ أَيُّهَآ أَزۡكَىٰ طَعَامٗا فَلۡيَأۡتِكُم بِرِزۡقٖ مِّنۡهُ وَلۡيَتَلَطَّفۡ وَلَا يُشۡعِرَنَّ بِكُمۡ أَحَدًا ﴾
[الكَهف: 19]
﴿وكذلك بعثناهم ليتساءلوا بينهم قال قائل منهم كم لبثتم قالوا لبثنا يوما﴾ [الكَهف: 19]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma kamar wannan ne Muka tayar da su, domin* su tambayi juna a tsakaninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mene ne lokacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sashen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin**. Sai ya duba wanne ne mafi tsarki ga abin dafawa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma kamar wannan ne Muka tayar da su, domin su tambayi juna a tsakaninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mene ne lokacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sashen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya duba wanne ne mafi tsarki ga abin dafawa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma kamar wannan ne Muka tãyar da su, dõmin su tambayi jũna a tsakãninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mẽne ne lõkacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sãshen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin. Sai ya dũba wanne ne mafi tsarki ga abin dafãwa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum |