Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 85 - البَقَرَة - Page - Juz 1
﴿ثُمَّ أَنتُمۡ هَٰٓؤُلَآءِ تَقۡتُلُونَ أَنفُسَكُمۡ وَتُخۡرِجُونَ فَرِيقٗا مِّنكُم مِّن دِيَٰرِهِمۡ تَظَٰهَرُونَ عَلَيۡهِم بِٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡعُدۡوَٰنِ وَإِن يَأۡتُوكُمۡ أُسَٰرَىٰ تُفَٰدُوهُمۡ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيۡكُمۡ إِخۡرَاجُهُمۡۚ أَفَتُؤۡمِنُونَ بِبَعۡضِ ٱلۡكِتَٰبِ وَتَكۡفُرُونَ بِبَعۡضٖۚ فَمَا جَزَآءُ مَن يَفۡعَلُ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ إِلَّا خِزۡيٞ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۖ وَيَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ يُرَدُّونَ إِلَىٰٓ أَشَدِّ ٱلۡعَذَابِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ ﴾
[البَقَرَة: 85]
﴿ثم أنتم هؤلاء تقتلون أنفسكم وتخرجون فريقا منكم من ديارهم تظاهرون عليهم﴾ [البَقَرَة: 85]
Abubakar Mahmood Jummi Sa'an nan kuma, ga ku, ya waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidajensu, kuna taimakon juna a kansu da zunubi da zalunci kuma idan kamammu suka je muku kuna fansarsu alhali kuwa shi fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna imani da sashen Littafin ne, kuma ku kafirta da sashe? To, mene ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku face wulakanci* a cikin rayuwar duniya? Kuma a Ranar ¡iyama ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan kuma, ga ku, ya waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidajensu, kuna taimakon juna a kansu da zunubi da zalunci kuma idan kamammu suka je muku kuna fansarsu alhali kuwa shi fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna imani da sashen Littafin ne, kuma ku kafirta da sashe? To, mene ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku face wulakanci a cikin rayuwar duniya? Kuma a Ranar ¡iyama ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan kuma, gã ku, yã waɗannan! Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidãjensu, kuna taimakon jũna a kansu da zunubi da zãlunci kuma idan kãmammu suka je muku kuna fansarsu alhãli kuwa shĩ fitar da su abin da aka haramta muku ne. Shin fa, kuna ĩmãni da sãshen Littãfin ne, kuma ku kãfirta da sãshe? To, mẽne ne sakamakon wanda ke aikata wancan daga gare ku fãce wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya? Kuma a Rãnar ¡iyãma ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azãba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatãwa |