Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 58 - النور - Page - Juz 18
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لِيَسۡتَـٔۡذِنكُمُ ٱلَّذِينَ مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ وَٱلَّذِينَ لَمۡ يَبۡلُغُواْ ٱلۡحُلُمَ مِنكُمۡ ثَلَٰثَ مَرَّٰتٖۚ مِّن قَبۡلِ صَلَوٰةِ ٱلۡفَجۡرِ وَحِينَ تَضَعُونَ ثِيَابَكُم مِّنَ ٱلظَّهِيرَةِ وَمِنۢ بَعۡدِ صَلَوٰةِ ٱلۡعِشَآءِۚ ثَلَٰثُ عَوۡرَٰتٖ لَّكُمۡۚ لَيۡسَ عَلَيۡكُمۡ وَلَا عَلَيۡهِمۡ جُنَاحُۢ بَعۡدَهُنَّۚ طَوَّٰفُونَ عَلَيۡكُم بَعۡضُكُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٖۚ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ لَكُمُ ٱلۡأٓيَٰتِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ ﴾
[النور: 58]
﴿ياأيها الذين آمنوا ليستأذنكم الذين ملكت أيمانكم والذين لم يبلغوا الحلم منكم﴾ [النور: 58]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Waɗannan da hannuwanku na dama suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nemi izni* sau uku; daga gabanin sallar alfijir da lokacin da kuke ajiye tufafinku saboda zafin rana, kuma daga bayan sallar isha'i. Su ne al'aurori uku a gare ku. Babu laifi a kanku kuma babu a kansu a bayansu. Su masu kewaya ne a kanku sashenku a kan sashe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ayoyin Sa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Waɗannan da hannuwanku na dama suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nemi izni sau uku; daga gabanin sallar alfijir da lokacin da kuke ajiye tufafinku saboda zafin rana, kuma daga bayan sallar isha'i. Su ne al'aurori uku a gare ku. Babu laifi a kanku kuma babu a kansu a bayansu. Su masu kewaya ne a kanku sashenku a kan sashe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ayoyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Waɗannan da hannuwanku na dãma suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nẽmi izni sau uku; daga gabãnin sallar alfijir da lõkacin da kuke ajiye tufãfinku sabõda zãfin rãnã, kuma daga bãyan sallar ishã'i. Sũ ne al'aurõri uku a gare ku. Bãbu laifi a kanku kuma bãbu a kansu a bãyansu. Sũ mãsu kẽwaya ne a kanku sãshenku a kan sãshe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima |