Quran with Hausa translation - Surah Yunus ayat 22 - يُونس - Page - Juz 11
﴿هُوَ ٱلَّذِي يُسَيِّرُكُمۡ فِي ٱلۡبَرِّ وَٱلۡبَحۡرِۖ حَتَّىٰٓ إِذَا كُنتُمۡ فِي ٱلۡفُلۡكِ وَجَرَيۡنَ بِهِم بِرِيحٖ طَيِّبَةٖ وَفَرِحُواْ بِهَا جَآءَتۡهَا رِيحٌ عَاصِفٞ وَجَآءَهُمُ ٱلۡمَوۡجُ مِن كُلِّ مَكَانٖ وَظَنُّوٓاْ أَنَّهُمۡ أُحِيطَ بِهِمۡ دَعَوُاْ ٱللَّهَ مُخۡلِصِينَ لَهُ ٱلدِّينَ لَئِنۡ أَنجَيۡتَنَا مِنۡ هَٰذِهِۦ لَنَكُونَنَّ مِنَ ٱلشَّٰكِرِينَ ﴾
[يُونس: 22]
﴿هو الذي يسيركم في البر والبحر حتى إذا كنتم في الفلك وجرين﴾ [يُونس: 22]
Abubakar Mahmood Jummi Shi ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) teku, sai idan kun kasance a cikin jirage, su gudana tare da su da iska mai daɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata guguwa ta je wa jiragen, kuma taguwar ruwa ta je musu daga kowane wuri, kuma su tabbata cewa su, an kewaye su, sai su kirayi Allah, suna masu tsarkake addini gare Shi, (suna cewa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙiƙa muna kasancewa daga masu godiya |
Abubakar Mahmoud Gumi Shi ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) teku, sai idan kun kasance a cikin jirage, su gudana tare da su da iska mai daɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata guguwa ta je wa jiragen, kuma taguwar ruwa ta je musu daga kowane wuri, kuma su tabbata cewa su, an kewaye su, sai su kirayi Allah, suna masu tsarkake addini gare Shi, (suna cewa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙiƙa muna kasancewa daga masu godiya |
Abubakar Mahmoud Gumi Shĩ ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) tẽku, sai idan kun kasance a cikin jirãge, su gudãna tãre da su da iska mai dãɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata gũguwa ta je wa jirãgen, kuma tãguwar ruwa ta jẽ musu daga kõwane wuri, kuma su tabbata cẽwa sũ, an kẽwaye su, sai su kirãyi Allah, sunã mãsu tsarkake addini gare Shi, (sunã cẽwa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙĩƙa munã kasancẽwa daga mãsu gõdiya |