Quran with Hausa translation - Surah Yusuf ayat 31 - يُوسُف - Page - Juz 12
﴿فَلَمَّا سَمِعَتۡ بِمَكۡرِهِنَّ أَرۡسَلَتۡ إِلَيۡهِنَّ وَأَعۡتَدَتۡ لَهُنَّ مُتَّكَـٔٗا وَءَاتَتۡ كُلَّ وَٰحِدَةٖ مِّنۡهُنَّ سِكِّينٗا وَقَالَتِ ٱخۡرُجۡ عَلَيۡهِنَّۖ فَلَمَّا رَأَيۡنَهُۥٓ أَكۡبَرۡنَهُۥ وَقَطَّعۡنَ أَيۡدِيَهُنَّ وَقُلۡنَ حَٰشَ لِلَّهِ مَا هَٰذَا بَشَرًا إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا مَلَكٞ كَرِيمٞ ﴾
[يُوسُف: 31]
﴿فلما سمعت بمكرهن أرسلت إليهن وأعتدت لهن متكأ وآتت كل واحدة منهن﴾ [يُوسُف: 31]
Abubakar Mahmood Jummi Sa'an nan a lokacin da ta ji labari game da makircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dogara wajen cinsa, kuma ta bai wa kowace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lokacin da, suka gan shi, suka girmama shi, kuma suka yanyanke hannayensu, kuma suka ce: "Tsarki yana ga Allah! Wannan ba mutum ba ne! Wannan bai zama ba face Mala'ika ne mai daraja |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan a lokacin da ta ji labari game da makircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dogara wajen cinsa, kuma ta bai wa kowace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lokacin da, suka gan shi, suka girmama shi, kuma suka yanyanke hannayensu, kuma suka ce: "Tsarki yana ga Allah! Wannan ba mutum ba ne! Wannan bai zama ba face Mala'ika ne mai daraja |
Abubakar Mahmoud Gumi Sa'an nan a lõkacin da ta ji lãbãri game da mãkircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dõgara wajen cinsa, kuma ta bai wa kõwace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lõkacin da, suka gan shi, suka girmamã shi, kuma suka yanyanke hannãyensu, kuma suka ce: "Tsarki yanã ga Allah! Wannan bã mutum ba ne! Wannan bai zama ba fãce Malã'ika ne mai daraja |