Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 143 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَكَذَٰلِكَ جَعَلۡنَٰكُمۡ أُمَّةٗ وَسَطٗا لِّتَكُونُواْ شُهَدَآءَ عَلَى ٱلنَّاسِ وَيَكُونَ ٱلرَّسُولُ عَلَيۡكُمۡ شَهِيدٗاۗ وَمَا جَعَلۡنَا ٱلۡقِبۡلَةَ ٱلَّتِي كُنتَ عَلَيۡهَآ إِلَّا لِنَعۡلَمَ مَن يَتَّبِعُ ٱلرَّسُولَ مِمَّن يَنقَلِبُ عَلَىٰ عَقِبَيۡهِۚ وَإِن كَانَتۡ لَكَبِيرَةً إِلَّا عَلَى ٱلَّذِينَ هَدَى ٱللَّهُۗ وَمَا كَانَ ٱللَّهُ لِيُضِيعَ إِيمَٰنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِٱلنَّاسِ لَرَءُوفٞ رَّحِيمٞ ﴾
[البَقَرَة: 143]
﴿وكذلك جعلناكم أمة وسطا لتكونوا شهداء على الناس ويكون الرسول عليكم شهيدا﴾ [البَقَرَة: 143]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya* domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla** wadda ka kasance a kanta ba, face domin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake juyawa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, ta kasance haƙiƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tozartar da imaninku.*** Lalle ne, Allah, ga mutane, haƙiƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya domin ku kasance masu bayar da shaida a kan mutane. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, face domin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake juyawa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, ta kasance haƙiƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tozartar da imaninku. Lalle ne, Allah, ga mutane, haƙiƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma kamar wancan, Muka sanya ku al'umma matsakaiciya dõmin ku kasance mãsu bãyar da shaida a kan mutãne. Kuma Manzo ya kasance mai shaida a kanku. Kuma ba Mu sanya Alƙibla wadda ka kasance a kanta ba, fãce dõmin Mu san wanda yake biyar Manzo daga wanda yake jũyãwa a kan duga-dugansa. Kuma lalle ne, tã kasance haƙĩƙa, mai girma, sai a kan waɗanda Allah Ya shiryar. Kuma ba ya yiwuwa ga Allah Ya tõzartar da ĩmãninku. Lalle ne, Allah, ga mutãne, haƙĩƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai |