Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 187 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿أُحِلَّ لَكُمۡ لَيۡلَةَ ٱلصِّيَامِ ٱلرَّفَثُ إِلَىٰ نِسَآئِكُمۡۚ هُنَّ لِبَاسٞ لَّكُمۡ وَأَنتُمۡ لِبَاسٞ لَّهُنَّۗ عَلِمَ ٱللَّهُ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَخۡتَانُونَ أَنفُسَكُمۡ فَتَابَ عَلَيۡكُمۡ وَعَفَا عَنكُمۡۖ فَٱلۡـَٰٔنَ بَٰشِرُوهُنَّ وَٱبۡتَغُواْ مَا كَتَبَ ٱللَّهُ لَكُمۡۚ وَكُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ حَتَّىٰ يَتَبَيَّنَ لَكُمُ ٱلۡخَيۡطُ ٱلۡأَبۡيَضُ مِنَ ٱلۡخَيۡطِ ٱلۡأَسۡوَدِ مِنَ ٱلۡفَجۡرِۖ ثُمَّ أَتِمُّواْ ٱلصِّيَامَ إِلَى ٱلَّيۡلِۚ وَلَا تُبَٰشِرُوهُنَّ وَأَنتُمۡ عَٰكِفُونَ فِي ٱلۡمَسَٰجِدِۗ تِلۡكَ حُدُودُ ٱللَّهِ فَلَا تَقۡرَبُوهَاۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ ٱللَّهُ ءَايَٰتِهِۦ لِلنَّاسِ لَعَلَّهُمۡ يَتَّقُونَ ﴾
[البَقَرَة: 187]
﴿أحل لكم ليلة الصيام الرفث إلى نسائكم هن لباس لكم وأنتم لباس﴾ [البَقَرَة: 187]
Abubakar Mahmood Jummi An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i* zuwa ga matanku su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karɓi tubarku, kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu itikafi a cikin masallatai. Waɗancan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi taƙawa |
Abubakar Mahmoud Gumi An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku su tufa ne a gare ku, kuma ku tufa ne a gare su, Allah Ya sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Saboda haka Ya karɓi tubarku, kuma Ya yafe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nemi abin da Allah ya rubuta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har silili fari ya bayyana a gare ku daga silili baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhali kuna masu itikafi a cikin masallatai. Waɗancan iyakokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ayoyinSa ga mutane: tsammaninsu, za su yi taƙawa |
Abubakar Mahmoud Gumi An halatta a gare ku, a daren azumi, yin jima'i zuwa ga matanku sũ tufa ne a gare ku, kuma kũ tufa ne a gare su, Allah Yã sani lalle ne ku kun kasance kuna yaudarar kanku. Sabõda haka Yã karɓi tũbarku, kuma Yã yãfe muku. To, yanzu ku rungume su kuma ku nẽmi abin da Allah yã rubũta muku. Kuma ku ci kuma ku sha har sĩlĩli fari ya bayyana a gare ku daga sĩlĩli baƙi daga alfijiri, sa'an nan kuma ku cika azumi zuwa ga dare. Kuma kada ku rungume su alhãli kuna mãsu itikãfi a cikin masallãtai. Waɗancan iyãkokin Allah ne: don haka kada ku kusancesu kamar haka ne Allah Yake bayyana ãyõyinSa ga mutãne: tsammãninsu, zã su yi taƙawa |