Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 217 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلشَّهۡرِ ٱلۡحَرَامِ قِتَالٖ فِيهِۖ قُلۡ قِتَالٞ فِيهِ كَبِيرٞۚ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ ٱللَّهِ وَكُفۡرُۢ بِهِۦ وَٱلۡمَسۡجِدِ ٱلۡحَرَامِ وَإِخۡرَاجُ أَهۡلِهِۦ مِنۡهُ أَكۡبَرُ عِندَ ٱللَّهِۚ وَٱلۡفِتۡنَةُ أَكۡبَرُ مِنَ ٱلۡقَتۡلِۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَٰتِلُونَكُمۡ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمۡ عَن دِينِكُمۡ إِنِ ٱسۡتَطَٰعُواْۚ وَمَن يَرۡتَدِدۡ مِنكُمۡ عَن دِينِهِۦ فَيَمُتۡ وَهُوَ كَافِرٞ فَأُوْلَٰٓئِكَ حَبِطَتۡ أَعۡمَٰلُهُمۡ فِي ٱلدُّنۡيَا وَٱلۡأٓخِرَةِۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ ﴾
[البَقَرَة: 217]
﴿يسألونك عن الشهر الحرام قتال فيه قل قتال فيه كبير وصد عن﴾ [البَقَرَة: 217]
Abubakar Mahmood Jummi Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yaki a cikinsa. Ka ce: "Yin yaƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kafirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutanensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma ba su gushewa suna yaƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhali kuwa yana kafiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓaci a cikin duniya da Lahira. Kuma waɗannan abokan Wuta ne, su a cikinta madawwama ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yaki a cikinsa. Ka ce: "Yin yaƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kafirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutanensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma ba su gushewa suna yaƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhali kuwa yana kafiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓaci a cikin duniya da Lahira. Kuma waɗannan abokan Wuta ne, su a cikinta madawwama ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne |