×

Kuma mãsu haifuwa (sakakku)* suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku 2:233 Hausa translation

Quran infoHausaSurah Al-Baqarah ⮕ (2:233) ayat 233 in Hausa

2:233 Surah Al-Baqarah ayat 233 in Hausa (الهوسا)

Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 233 - البَقَرَة - Page - Juz 2

﴿۞ وَٱلۡوَٰلِدَٰتُ يُرۡضِعۡنَ أَوۡلَٰدَهُنَّ حَوۡلَيۡنِ كَامِلَيۡنِۖ لِمَنۡ أَرَادَ أَن يُتِمَّ ٱلرَّضَاعَةَۚ وَعَلَى ٱلۡمَوۡلُودِ لَهُۥ رِزۡقُهُنَّ وَكِسۡوَتُهُنَّ بِٱلۡمَعۡرُوفِۚ لَا تُكَلَّفُ نَفۡسٌ إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَا تُضَآرَّ وَٰلِدَةُۢ بِوَلَدِهَا وَلَا مَوۡلُودٞ لَّهُۥ بِوَلَدِهِۦۚ وَعَلَى ٱلۡوَارِثِ مِثۡلُ ذَٰلِكَۗ فَإِنۡ أَرَادَا فِصَالًا عَن تَرَاضٖ مِّنۡهُمَا وَتَشَاوُرٖ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡهِمَاۗ وَإِنۡ أَرَدتُّمۡ أَن تَسۡتَرۡضِعُوٓاْ أَوۡلَٰدَكُمۡ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ إِذَا سَلَّمۡتُم مَّآ ءَاتَيۡتُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٞ ﴾
[البَقَرَة: 233]

Kuma mãsu haifuwa (sakakku)* suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne

❮ Previous Next ❯

ترجمة: والوالدات يرضعن أولادهن حولين كاملين لمن أراد أن يتم الرضاعة وعلى المولود, باللغة الهوسا

﴿والوالدات يرضعن أولادهن حولين كاملين لمن أراد أن يتم الرضاعة وعلى المولود﴾ [البَقَرَة: 233]

Abubakar Mahmood Jummi
Kuma masu haifuwa (sakakku)* suna shayar da abin haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alheri. Ba a kallafa wa rai face iyawarsa. Ba a cutar da uwa game da ɗanta, kuma ba a cutar da uba game da ɗansa, kuma a kan magaji akwai misalin wancan. To, idan suka yi nufin yaye, a kan yardatayya daga gare su, da shawartar juna, to babu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bayar da ɗiyanku shayarwa, to, babu laifi a kanku idan kun miƙa abin da kukazo da shi bisa al'ada. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne
Abubakar Mahmoud Gumi
Kuma masu haifuwa (sakakku) suna shayar da abin haifuwarsu shekara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shayarwa. Kuma ciyar da su da tufatar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alheri. Ba a kallafa wa rai face iyawarsa. Ba a cutar da uwa game da ɗanta, kuma ba a cutar da uba game da ɗansa, kuma a kan magaji akwai misalin wancan. To, idan suka yi nufin yaye, a kan yardatayya daga gare su, da shawartar juna, to babu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bayar da ɗiyanku shayarwa, to, babu laifi a kanku idan kun miƙa abin da kukazo da shi bisa al'ada. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cewa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne
Abubakar Mahmoud Gumi
Kuma mãsu haifuwa (sakakku) suna shãyar da abin haifuwarsu shẽkara biyu cikakku ga wanda ya yi nufin ya cika shãyarwa. Kuma ciyar da su da tufãtar da su yana a kan wanda aka haifar masa da alhẽri. Bã a kallafa wa rai fãce iyãwarsa. Bã a cũtar da uwa game da ɗanta, kuma bã a cũtar da uba game da ɗansa, kuma a kan magãji akwai misãlin wancan. To, idan suka yi nufin yãye, a kan yardatayya daga gare su, da shãwartar jũna, to bãbu laifi a kansu. Kuma idan, kun yi nufin ku bãyar da ɗiyanku shãyarwa, to, bãbu laifi a kanku idan kun mĩƙa abin da kukazo da shi bisa al'ãda. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle ne Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne
❮ Previous Next ❯

Verse in more languages

Transliteration Bangla Bosnian German English Persian French Hindi Indonesian Kazakh Dutch Russian Spanish Turkish Urdu Uzbek