Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 232 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَإِذَا طَلَّقۡتُمُ ٱلنِّسَآءَ فَبَلَغۡنَ أَجَلَهُنَّ فَلَا تَعۡضُلُوهُنَّ أَن يَنكِحۡنَ أَزۡوَٰجَهُنَّ إِذَا تَرَٰضَوۡاْ بَيۡنَهُم بِٱلۡمَعۡرُوفِۗ ذَٰلِكَ يُوعَظُ بِهِۦ مَن كَانَ مِنكُمۡ يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِۗ ذَٰلِكُمۡ أَزۡكَىٰ لَكُمۡ وَأَطۡهَرُۚ وَٱللَّهُ يَعۡلَمُ وَأَنتُمۡ لَا تَعۡلَمُونَ ﴾
[البَقَرَة: 232]
﴿وإذا طلقتم النساء فبلغن أجلهن فلا تعضلوهن أن ينكحن أزواجهن إذا تراضوا﴾ [البَقَرَة: 232]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan kuka saki mata, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da juna a tsakaninsu (tsohon miji da tsohuwar mata) da alheri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana imani da Allah da Ranar Lahira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma ku ba ku sani ba |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kuka saki mata, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da juna a tsakaninsu (tsohon miji da tsohuwar mata) da alheri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana imani da Allah da Ranar Lahira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma ku ba ku sani ba |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kuka saki mãta, har suka isa ga ajalinsu (iddarsu), to, kada ku (waliyyansu) hana su, su auri mazansu (da suka sake su) idan sun yarda da jũna a tsakãninsu (tsõhon miji da tsõhuwar mãta) da alhẽri. Wancan ana yin wa'azi da shi ga wanda ya kasance daga gare ku yana ĩmãni da Allah da Rãnar Lãhira. Wancan ne mafi mutunci a gare ku, kuma mafi tsarki. Kuma Allah Yana sani, kuma kũ ba ku sani ba |