Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 237 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَإِن طَلَّقۡتُمُوهُنَّ مِن قَبۡلِ أَن تَمَسُّوهُنَّ وَقَدۡ فَرَضۡتُمۡ لَهُنَّ فَرِيضَةٗ فَنِصۡفُ مَا فَرَضۡتُمۡ إِلَّآ أَن يَعۡفُونَ أَوۡ يَعۡفُوَاْ ٱلَّذِي بِيَدِهِۦ عُقۡدَةُ ٱلنِّكَاحِۚ وَأَن تَعۡفُوٓاْ أَقۡرَبُ لِلتَّقۡوَىٰۚ وَلَا تَنسَوُاْ ٱلۡفَضۡلَ بَيۡنَكُمۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرٌ ﴾
[البَقَرَة: 237]
﴿وإن طلقتموهن من قبل أن تمسوهن وقد فرضتم لهن فريضة فنصف ما﴾ [البَقَرَة: 237]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan kuka sake su daga gabanin ku shafe su, alhali kuwa* kun yanka musu sadaki, to, rabin abin da kuka yanka face idan sun yafe, ko wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yafe. Kuma ku yafe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakaninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kuka sake su daga gabanin ku shafe su, alhali kuwa kun yanka musu sadaki, to, rabin abin da kuka yanka face idan sun yafe, ko wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yafe. Kuma ku yafe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakaninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatawa Mai gani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan kuka sake su daga gabãnin ku shãfe su, alhãli kuwa kun yanka musu sadãki, to, rabin abin da kuka yanka fãce idan sun yãfe, kõ wanda ɗaurin auren yake ga hannunsa ya yãfe. Kuma ku yãfe ɗin ne mafi kusa da taƙawa. Kuma kada ku manta da falala a tsakãninku. Lalle ne Allah ga abin da kuke aikatãwa Mai gani ne |