Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 240 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿وَٱلَّذِينَ يُتَوَفَّوۡنَ مِنكُمۡ وَيَذَرُونَ أَزۡوَٰجٗا وَصِيَّةٗ لِّأَزۡوَٰجِهِم مَّتَٰعًا إِلَى ٱلۡحَوۡلِ غَيۡرَ إِخۡرَاجٖۚ فَإِنۡ خَرَجۡنَ فَلَا جُنَاحَ عَلَيۡكُمۡ فِي مَا فَعَلۡنَ فِيٓ أَنفُسِهِنَّ مِن مَّعۡرُوفٖۗ وَٱللَّهُ عَزِيزٌ حَكِيمٞ ﴾
[البَقَرَة: 240]
﴿والذين يتوفون منكم ويذرون أزواجا وصية لأزواجهم متاعا إلى الحول غير إخراج﴾ [البَقَرَة: 240]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma waɗanda suke mutuwa* daga gare ku, alhali suna barin matan aure, wasiyya ga matan aurensu da daɗaɗawa zuwa ga shekara guda babu fitarwa, to, idan sun fita to babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku, alhali suna barin matan aure, wasiyya ga matan aurensu da daɗaɗawa zuwa ga shekara guda babu fitarwa, to, idan sun fita to babu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗanda suke mutuwa daga gare ku, alhãli suna barin mãtan aure, wasiyya ga mãtan aurensu da dãɗaɗãwa zuwa ga shekara guda bãbu fitarwa, to, idan sun fita to bãbu laifi a kanku a cikin abin da suka aikata game da kansu daga abin da aka sani, kuma Allah Mabuwayi ne, Mai hikima |