Quran with Hausa translation - Surah Al-Mu’minun ayat 27 - المؤمنُون - Page - Juz 18
﴿فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ أَنِ ٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ فَٱسۡلُكۡ فِيهَا مِن كُلّٖ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ مِنۡهُمۡۖ وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ ﴾
[المؤمنُون: 27]
﴿فأوحينا إليه أن اصنع الفلك بأعيننا ووحينا فإذا جاء أمرنا وفار التنور﴾ [المؤمنُون: 27]
Abubakar Mahmood Jummi Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya je, kuma tanda ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kome, ma'aura biyu, da iyalanka, sai wanda Magana ta gabata a kansa, daga gare su, kuma kada ka roƙe Ni (saboda wani) a cikin waɗanda suka yi zalunci, lalle ne su waɗanda ake nutsarwa ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya je, kuma tanda ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kome, ma'aura biyu, da iyalanka, sai wanda Magana ta gabata a kansa, daga gare su, kuma kada ka roƙe Ni (saboda wani) a cikin waɗanda suka yi zalunci, lalle ne su waɗanda ake nutsarwa ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne |