Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 31 - النور - Page - Juz 18
﴿وَقُل لِّلۡمُؤۡمِنَٰتِ يَغۡضُضۡنَ مِنۡ أَبۡصَٰرِهِنَّ وَيَحۡفَظۡنَ فُرُوجَهُنَّ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا مَا ظَهَرَ مِنۡهَاۖ وَلۡيَضۡرِبۡنَ بِخُمُرِهِنَّ عَلَىٰ جُيُوبِهِنَّۖ وَلَا يُبۡدِينَ زِينَتَهُنَّ إِلَّا لِبُعُولَتِهِنَّ أَوۡ ءَابَآئِهِنَّ أَوۡ ءَابَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآئِهِنَّ أَوۡ أَبۡنَآءِ بُعُولَتِهِنَّ أَوۡ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ إِخۡوَٰنِهِنَّ أَوۡ بَنِيٓ أَخَوَٰتِهِنَّ أَوۡ نِسَآئِهِنَّ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُنَّ أَوِ ٱلتَّٰبِعِينَ غَيۡرِ أُوْلِي ٱلۡإِرۡبَةِ مِنَ ٱلرِّجَالِ أَوِ ٱلطِّفۡلِ ٱلَّذِينَ لَمۡ يَظۡهَرُواْ عَلَىٰ عَوۡرَٰتِ ٱلنِّسَآءِۖ وَلَا يَضۡرِبۡنَ بِأَرۡجُلِهِنَّ لِيُعۡلَمَ مَا يُخۡفِينَ مِن زِينَتِهِنَّۚ وَتُوبُوٓاْ إِلَى ٱللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ لَعَلَّكُمۡ تُفۡلِحُونَ ﴾
[النور: 31]
﴿وقل للمؤمنات يغضضن من أبصارهن ويحفظن فروجهن ولا يبدين زينتهن إلا ما﴾ [النور: 31]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna ƙawarsu face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mata, ko matan* ƙungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai waɗanda. ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da ƙafafunsu domin a san abin da suke ɓoyewa daga ƙawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna ƙawarsu face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mata, ko matan ƙungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai waɗanda. ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da ƙafafunsu domin a san abin da suke ɓoyewa daga ƙawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka ce wa mũminai mãta su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjõjinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu fãce abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su dõka da mayãfansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nũna ƙawarsu fãce ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mãtã, kõ mãtan ƙungiyarsu, ko abin da hannãyensu na dãma suka mallaka, ko mabiya wasun mãsu bukãtar mãta daga maza, kõ jãrirai waɗanda. bã su tsinkãya a kan al'aurar mãtã. Kuma kada su yi dũka da ƙafãfunsu dõmin a san abin da suke ɓõyẽwa daga ƙawarsu. Kuma ku tũba zuwa ga Allah gabã ɗaya, yã ku mũminai! Tsammãninku, ku sãmi babban rabo |