Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 33 - النور - Page - Juz 18
﴿وَلۡيَسۡتَعۡفِفِ ٱلَّذِينَ لَا يَجِدُونَ نِكَاحًا حَتَّىٰ يُغۡنِيَهُمُ ٱللَّهُ مِن فَضۡلِهِۦۗ وَٱلَّذِينَ يَبۡتَغُونَ ٱلۡكِتَٰبَ مِمَّا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُكُمۡ فَكَاتِبُوهُمۡ إِنۡ عَلِمۡتُمۡ فِيهِمۡ خَيۡرٗاۖ وَءَاتُوهُم مِّن مَّالِ ٱللَّهِ ٱلَّذِيٓ ءَاتَىٰكُمۡۚ وَلَا تُكۡرِهُواْ فَتَيَٰتِكُمۡ عَلَى ٱلۡبِغَآءِ إِنۡ أَرَدۡنَ تَحَصُّنٗا لِّتَبۡتَغُواْ عَرَضَ ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَاۚ وَمَن يُكۡرِههُّنَّ فَإِنَّ ٱللَّهَ مِنۢ بَعۡدِ إِكۡرَٰهِهِنَّ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ﴾
[النور: 33]
﴿وليستعفف الذين لا يجدون نكاحا حتى يغنيهم الله من فضله والذين يبتغون﴾ [النور: 33]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma waɗannan da ba su sami aure ba su kame kansu har Allah Ya wadatar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke neman fansa daga abin da hannuwanku na dama suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansa idan kun san akwai wani alheri a cikinsu kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah wannan da Ya ba ku. Kuma kada ku tilasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,* domin ku nemi rayuwar duniya, kuma wanda ya tilasta su to, lalle Allah, a bayan tilasta su, Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗannan da ba su sami aure ba su kame kansu har Allah Ya wadatar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke neman fansa daga abin da hannuwanku na dama suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansa idan kun san akwai wani alheri a cikinsu kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah wannan da Ya ba ku. Kuma kada ku tilasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, domin ku nemi rayuwar duniya, kuma wanda ya tilasta su to, lalle Allah, a bayan tilasta su, Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma waɗannan da ba su sãmi aure ba su kãme kansu har Allah Ya wadãtar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke nẽman fansa daga abin da hannuwanku na dãma suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansã idan kun san akwai wani alhẽri a cikinsu kuma ku bã su wani abu daga dũkiyar Allah wannan da Ya bã ku. Kuma kada ku tĩlasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu, dõmin ku nẽmi rãyuwar dũniya, kuma wanda ya tĩlasta su to, lalle Allah, a bãyan tĩlasta su, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |