Quran with Hausa translation - Surah An-Nur ayat 35 - النور - Page - Juz 18
﴿۞ ٱللَّهُ نُورُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ مَثَلُ نُورِهِۦ كَمِشۡكَوٰةٖ فِيهَا مِصۡبَاحٌۖ ٱلۡمِصۡبَاحُ فِي زُجَاجَةٍۖ ٱلزُّجَاجَةُ كَأَنَّهَا كَوۡكَبٞ دُرِّيّٞ يُوقَدُ مِن شَجَرَةٖ مُّبَٰرَكَةٖ زَيۡتُونَةٖ لَّا شَرۡقِيَّةٖ وَلَا غَرۡبِيَّةٖ يَكَادُ زَيۡتُهَا يُضِيٓءُ وَلَوۡ لَمۡ تَمۡسَسۡهُ نَارٞۚ نُّورٌ عَلَىٰ نُورٖۚ يَهۡدِي ٱللَّهُ لِنُورِهِۦ مَن يَشَآءُۚ وَيَضۡرِبُ ٱللَّهُ ٱلۡأَمۡثَٰلَ لِلنَّاسِۗ وَٱللَّهُ بِكُلِّ شَيۡءٍ عَلِيمٞ ﴾
[النور: 35]
﴿الله نور السموات والأرض مثل نوره كمشكاة فيها مصباح المصباح في زجاجة﴾ [النور: 35]
Abubakar Mahmood Jummi Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misalin HaskenSa, kamar taga, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi tauraro ne mai tsananin haske, ana kunna shi daga wata itaciya mai albarka, ta zaituni, ba bagabashiya ba kuma ba bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma ko wuta ba ta shafe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misalai ga mutane, kuma Allah game da dukan kome, Masani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misalin HaskenSa, kamar taga, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi tauraro ne mai tsananin haske, ana kunna shi daga wata itaciya mai albarka, ta zaituni, ba bagabashiya ba kuma ba bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma ko wuta ba ta shafe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misalai ga mutane, kuma Allah game da dukan kome, Masani ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misãlin HaskenSa, kamar tãgã, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi taurãro ne mai tsananin haske, anã kunna shi daga wata itãciya mai albarka, ta zaitũni, bã bagabashiya ba kuma bã bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma kõ wuta ba ta shãfe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misãlai ga mutãne, kuma Allah game da dukan kõme, Masani ne |