Quran with Hausa translation - Surah al-‘Imran ayat 110 - آل عِمران - Page - Juz 4
﴿كُنتُمۡ خَيۡرَ أُمَّةٍ أُخۡرِجَتۡ لِلنَّاسِ تَأۡمُرُونَ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَتَنۡهَوۡنَ عَنِ ٱلۡمُنكَرِ وَتُؤۡمِنُونَ بِٱللَّهِۗ وَلَوۡ ءَامَنَ أَهۡلُ ٱلۡكِتَٰبِ لَكَانَ خَيۡرٗا لَّهُمۚ مِّنۡهُمُ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَأَكۡثَرُهُمُ ٱلۡفَٰسِقُونَ ﴾
[آل عِمران: 110]
﴿كنتم خير أمة أخرجت للناس تأمرون بالمعروف وتنهون عن المنكر وتؤمنون بالله﴾ [آل عِمران: 110]
Abubakar Mahmood Jummi Kun kasance mafi alherin al'umma wadda aka fitar ga mutane kuna umurni da alheri kuma kuna hani daga abin da ake ƙi, kuma kuna imani da Allah. Kuma da Mutanen Littafi sun yi imani, lalle ne, da (haka) ya kasance mafi alheri a gare su. Daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawan su fasiƙai ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kun kasance mafi alherin al'umma wadda aka fitar ga mutane kuna umurni da alheri kuma kuna hani daga abin da ake ƙi, kuma kuna imani da Allah. Kuma da Mutanen Littafi sun yi imani, lalle ne, da (haka) ya kasance mafi alheri a gare su. Daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawansufasiƙai ne |
Abubakar Mahmoud Gumi Kun kasance mafi alhẽrin al'umma wadda aka fitar ga mutãne kuna umurni da alhẽri kuma kunã hani daga abin da ake ƙi, kuma kunã ĩmãni da Allah. Kuma dã Mutãnen Littãfi sun yi ĩmãni, lalle ne, dã (haka) yã kasance mafi alhẽri a gare su. Daga cikinsu akwai mũminai, kuma mafi yawansufãsiƙai ne |