Quran with Hausa translation - Surah Al-Ahzab ayat 37 - الأحزَاب - Page - Juz 22
﴿وَإِذۡ تَقُولُ لِلَّذِيٓ أَنۡعَمَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ وَأَنۡعَمۡتَ عَلَيۡهِ أَمۡسِكۡ عَلَيۡكَ زَوۡجَكَ وَٱتَّقِ ٱللَّهَ وَتُخۡفِي فِي نَفۡسِكَ مَا ٱللَّهُ مُبۡدِيهِ وَتَخۡشَى ٱلنَّاسَ وَٱللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخۡشَىٰهُۖ فَلَمَّا قَضَىٰ زَيۡدٞ مِّنۡهَا وَطَرٗا زَوَّجۡنَٰكَهَا لِكَيۡ لَا يَكُونَ عَلَى ٱلۡمُؤۡمِنِينَ حَرَجٞ فِيٓ أَزۡوَٰجِ أَدۡعِيَآئِهِمۡ إِذَا قَضَوۡاْ مِنۡهُنَّ وَطَرٗاۚ وَكَانَ أَمۡرُ ٱللَّهِ مَفۡعُولٗا ﴾
[الأحزَاب: 37]
﴿وإذ تقول للذي أنعم الله عليه وأنعمت عليه أمسك عليك زوجك واتق﴾ [الأحزَاب: 37]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma a lokacin* da kake cewa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe matarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓoyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi,** kana tsoron mutane, alhali kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsoronSa. to a lokacin da zaidu ya ƙare bukatarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, domin kada wani ƙunci ya kasance a kan muminai a cikin (auren matan) ɗiyan hankakarsu, idan sun ƙare bukata daga gare su. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lokacin da kake cewa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe matarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓoyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kana tsoron mutane, alhali kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsoronSa. to a lokacin da zaidu ya ƙare bukatarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, domin kada wani ƙunci ya kasance a kan muminai a cikin (auren matan) ɗiyan hankakarsu, idan sun ƙare bukata daga gare su. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lõkacin da kake cẽwa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe mãtarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓõyẽwa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi, kanã tsõron mutãne, alhãli kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsõronSa. to a lõkacin da zaidu ya ƙãre bukãtarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, dõmin kada wani ƙunci ya kasance a kan mũminai a cikin (auren mãtan) ɗiyan hankãkarsu, idan sun ƙãre bukãta daga gare su. Kuma umurnin Allah yã kasance abin aikatãwa |