Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 135 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿۞ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُونُواْ قَوَّٰمِينَ بِٱلۡقِسۡطِ شُهَدَآءَ لِلَّهِ وَلَوۡ عَلَىٰٓ أَنفُسِكُمۡ أَوِ ٱلۡوَٰلِدَيۡنِ وَٱلۡأَقۡرَبِينَۚ إِن يَكُنۡ غَنِيًّا أَوۡ فَقِيرٗا فَٱللَّهُ أَوۡلَىٰ بِهِمَاۖ فَلَا تَتَّبِعُواْ ٱلۡهَوَىٰٓ أَن تَعۡدِلُواْۚ وَإِن تَلۡوُۥٓاْ أَوۡ تُعۡرِضُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ كَانَ بِمَا تَعۡمَلُونَ خَبِيرٗا ﴾
[النِّسَاء: 135]
﴿ياأيها الذين آمنوا كونوا قوامين بالقسط شهداء لله ولو على أنفسكم أو﴾ [النِّسَاء: 135]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida* saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Saboda haka, kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Saboda haka, kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kasance mãsu tsayuwa da ãdalci, mãsu shaida sabõda Allah, kuma kõ dã a kanku ne kõ kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida kõ a kansa) ya kasance mawadãci kõ matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Sabõda haka, kada ku bĩbiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, kõ kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Yã kasance Masani ga abin da kuke aikatãwa |