Quran with Hausa translation - Surah An-Nisa’ ayat 83 - النِّسَاء - Page - Juz 5
﴿وَإِذَا جَآءَهُمۡ أَمۡرٞ مِّنَ ٱلۡأَمۡنِ أَوِ ٱلۡخَوۡفِ أَذَاعُواْ بِهِۦۖ وَلَوۡ رَدُّوهُ إِلَى ٱلرَّسُولِ وَإِلَىٰٓ أُوْلِي ٱلۡأَمۡرِ مِنۡهُمۡ لَعَلِمَهُ ٱلَّذِينَ يَسۡتَنۢبِطُونَهُۥ مِنۡهُمۡۗ وَلَوۡلَا فَضۡلُ ٱللَّهِ عَلَيۡكُمۡ وَرَحۡمَتُهُۥ لَٱتَّبَعۡتُمُ ٱلشَّيۡطَٰنَ إِلَّا قَلِيلٗا ﴾
[النِّسَاء: 83]
﴿وإذا جاءهم أمر من الأمن أو الخوف أذاعوا به ولو ردوه إلى﴾ [النِّسَاء: 83]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma idan wani al'amari* daga aminci ko tsoro ya je musu, sai su watsa shi. Da sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abuta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, za su san shi. Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamar Sa, haƙiƙa, da kun bi Shaiɗan face kaɗan |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsoro ya je musu, sai su watsa shi. Da sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abuta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, za su san shi. Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, haƙiƙa, da kun bi Shaiɗan face kaɗan |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma idan wani al'amari daga aminci ko tsõro ya je musu, sai su wãtsa shi. Dã sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abũta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, zã su san shi. Kuma bã dõmin falalar Allah bã a kanku da rahamarSa, haƙĩƙa, dã kun bi Shaiɗan fãce kaɗan |