Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 106 - المَائدة - Page - Juz 7
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ شَهَٰدَةُ بَيۡنِكُمۡ إِذَا حَضَرَ أَحَدَكُمُ ٱلۡمَوۡتُ حِينَ ٱلۡوَصِيَّةِ ٱثۡنَانِ ذَوَا عَدۡلٖ مِّنكُمۡ أَوۡ ءَاخَرَانِ مِنۡ غَيۡرِكُمۡ إِنۡ أَنتُمۡ ضَرَبۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَأَصَٰبَتۡكُم مُّصِيبَةُ ٱلۡمَوۡتِۚ تَحۡبِسُونَهُمَا مِنۢ بَعۡدِ ٱلصَّلَوٰةِ فَيُقۡسِمَانِ بِٱللَّهِ إِنِ ٱرۡتَبۡتُمۡ لَا نَشۡتَرِي بِهِۦ ثَمَنٗا وَلَوۡ كَانَ ذَا قُرۡبَىٰ وَلَا نَكۡتُمُ شَهَٰدَةَ ٱللَّهِ إِنَّآ إِذٗا لَّمِنَ ٱلۡأٓثِمِينَ ﴾
[المَائدة: 106]
﴿ياأيها الذين آمنوا شهادة بينكم إذا حضر أحدكم الموت حين الوصية اثنان﴾ [المَائدة: 106]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Shaidar* tsakaninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lokacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta adalci daga gare ku, ko kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masifar mutuwa ta same ku. Kuna tsare su daga bayan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Ba mu sayen kuɗi da shi, ko da ya kasance ma'abucin zumunta kuma ba mu ɓoye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lokacin, haƙiƙa, muna daga masu zunubi |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Shaidar tsakaninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lokacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta adalci daga gare ku, ko kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masifarmutuwa ta same ku. Kuna tsare su daga bayan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Ba mu sayen kuɗi da shi, ko da ya kasance ma'abucin zumunta kuma ba mu ɓoye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lokacin, haƙiƙa, muna daga masu zunubi |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Shaidar tsakãninku, idan mutuwa ta halarci ɗayanku, a lõkacin wasiyya, maza biyu ne ma'abuta ãdalci daga gare ku, kõ kuwa wasu biyu daga wasunku idan kun tafi a cikin ƙasa sa'an nan masĩfarmutuwa ta sãme ku. Kunã tsare su daga bãyan salla har su yi rantsuwa da Allah; idan kun yi shakka: "Bã mu sayen kuɗi da shi, kõ dã ya kasance ma'abucin zumunta kuma bã mu ɓõye shaidar Allah. Lalle ne mu, a lõkacin, haƙĩƙa, munã daga mãsu zunubi |