Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 12 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿۞ وَلَقَدۡ أَخَذَ ٱللَّهُ مِيثَٰقَ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ وَبَعَثۡنَا مِنۡهُمُ ٱثۡنَيۡ عَشَرَ نَقِيبٗاۖ وَقَالَ ٱللَّهُ إِنِّي مَعَكُمۡۖ لَئِنۡ أَقَمۡتُمُ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَيۡتُمُ ٱلزَّكَوٰةَ وَءَامَنتُم بِرُسُلِي وَعَزَّرۡتُمُوهُمۡ وَأَقۡرَضۡتُمُ ٱللَّهَ قَرۡضًا حَسَنٗا لَّأُكَفِّرَنَّ عَنكُمۡ سَيِّـَٔاتِكُمۡ وَلَأُدۡخِلَنَّكُمۡ جَنَّٰتٖ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ فَمَن كَفَرَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ مِنكُمۡ فَقَدۡ ضَلَّ سَوَآءَ ٱلسَّبِيلِ ﴾
[المَائدة: 12]
﴿ولقد أخذ الله ميثاق بني إسرائيل وبعثنا منهم اثني عشر نقيبا وقال﴾ [المَائدة: 12]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma lalle Allah Ya riƙi alkawarin Bani lsra' ila kuma Muka ayyana wakilai goma sha biyu* daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Ni, Ina tare da ku, haƙiƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bayar da zakka, kuma kun yi imani da manzanni Na, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙiƙa, Ina kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙiƙa, Ina shigar da ku gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu sana gudana a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kafirta a bayan wannan daga gare ku, to, lalle ne, ya ɓace daga tsakar hanya |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma lalle Allah Ya riƙi alkawarin Bani lsra' ila kuma Muka ayyana wakilai goma sha biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Ni, Ina tare da ku, haƙiƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bayar da zakka, kuma kun yi imani da manzanniNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙiƙa, Ina kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙiƙa, Ina shigar da ku gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu sana gudana a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kafirta a bayan wannan daga gare ku, to, lalle ne, ya ɓace daga tsakar hanya |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma lalle Allah Yã riƙi alkawarin Banĩ lsrã' ĩla kuma Muka ayyana wakilai gõma shã biyu daga gare su kuma Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ, Inã tãre da ku, haƙĩƙa, idan kun tsayar da salla, kuma kun bãyar da zakka, kuma kun yi ĩmani da manzannĩNa, kuma kuka taimake su, kuma kuka bai wa Allah rance mai kyau, haƙĩƙa, Inã kankare laifukanku daga gare ku, kuma haƙĩƙa, Inã shigar da ku gidãjen Aljanna (waɗanda) ƙõramu sanã gudãna a ƙarƙashinsu, sa'an nan wanda ya kãfirta a bãyan wannan daga gare ku, to, lalle ne, yã ɓace daga tsakar hanya |