Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 13 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿فَبِمَا نَقۡضِهِم مِّيثَٰقَهُمۡ لَعَنَّٰهُمۡ وَجَعَلۡنَا قُلُوبَهُمۡ قَٰسِيَةٗۖ يُحَرِّفُونَ ٱلۡكَلِمَ عَن مَّوَاضِعِهِۦ وَنَسُواْ حَظّٗا مِّمَّا ذُكِّرُواْ بِهِۦۚ وَلَا تَزَالُ تَطَّلِعُ عَلَىٰ خَآئِنَةٖ مِّنۡهُمۡ إِلَّا قَلِيلٗا مِّنۡهُمۡۖ فَٱعۡفُ عَنۡهُمۡ وَٱصۡفَحۡۚ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ ﴾
[المَائدة: 13]
﴿فبما نقضهم ميثاقهم لعناهم وجعلنا قلوبهم قاسية يحرفون الكلم عن مواضعه ونسوا﴾ [المَائدة: 13]
Abubakar Mahmood Jummi To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukatansu ƙeƙasassu, suna karkatar da magana daga wurarenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunatar da su da shi, kuma ba za ka gushe ba kana tsinkayar yaudara daga gare su face kaɗan daga gare su. To, ka yafe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yana son masu kyautatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukatansu ƙeƙasassu, suna karkatar da magana daga wurarenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunatar da su da shi, kuma ba za ka gushe ba kana tsinkayar yaudara daga gare su face kaɗan daga gare su. To, ka yafe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yana son masu kyautatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi To, sabõda warwarewarsu ga alkawarinsu Muka la'ane su, kuma Muka sanya zukãtansu ƙeƙasassu, sunã karkatar da magana daga wurãrenta, kuma suka manta da wani yanki daga abin da aka tunãtar da su da shi, kuma bã zã ka gushe ba kana tsinkãyar yaudara daga gare su fãce kaɗan daga gare su. To, ka yãfe laifi daga gare su, kuma ka kau da kai. Lalle ne, Allah Yanã son mãsu kyautatãwa |