Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 3 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿حُرِّمَتۡ عَلَيۡكُمُ ٱلۡمَيۡتَةُ وَٱلدَّمُ وَلَحۡمُ ٱلۡخِنزِيرِ وَمَآ أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦ وَٱلۡمُنۡخَنِقَةُ وَٱلۡمَوۡقُوذَةُ وَٱلۡمُتَرَدِّيَةُ وَٱلنَّطِيحَةُ وَمَآ أَكَلَ ٱلسَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيۡتُمۡ وَمَا ذُبِحَ عَلَى ٱلنُّصُبِ وَأَن تَسۡتَقۡسِمُواْ بِٱلۡأَزۡلَٰمِۚ ذَٰلِكُمۡ فِسۡقٌۗ ٱلۡيَوۡمَ يَئِسَ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن دِينِكُمۡ فَلَا تَخۡشَوۡهُمۡ وَٱخۡشَوۡنِۚ ٱلۡيَوۡمَ أَكۡمَلۡتُ لَكُمۡ دِينَكُمۡ وَأَتۡمَمۡتُ عَلَيۡكُمۡ نِعۡمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ ٱلۡإِسۡلَٰمَ دِينٗاۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ فِي مَخۡمَصَةٍ غَيۡرَ مُتَجَانِفٖ لِّإِثۡمٖ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ﴾
[المَائدة: 3]
﴿حرمت عليكم الميتة والدم ولحم الخنـزير وما أهل لغير الله به والمنخنقة﴾ [المَائدة: 3]
Abubakar Mahmood Jummi An haramta muku mushe da jini da naman alade da abin da aka ambaci sunan wanin Allah a gare shi, da maƙararriya da jefaffiya da mai gangarowa da sokakkiya, da abin da masu dagi suka ci, face abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shi ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na caca wannan fasiƙanci ne, A yau waɗanda suka kafirta sun yanke ƙauna daga addininku. Saboda haka kada ku ji tsoronsu kuma ku ji tsoroNa. A yau Na kammala muku addininku, Kuma Na cika ni'imaTa a kanku, Kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalura a cikin yunwa mai tsanani, ba yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi An haramta muku mushe da jini da naman alade da abin da aka ambaci sunan wanin Allah a gare shi, da maƙararriya da jefaffiya da mai gangarowa da sokakkiya, da abin da masu dagi suka ci, face abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shi ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na caca wannan fasiƙanci ne, A yau waɗanda suka kafirta sun yanke ƙauna daga addininku. Saboda haka kada ku ji tsoronsu kuma ku ji tsoroNa. A yau Na kammala muku addininku, Kuma Na cika ni'imaTa a kanku, Kuma Na yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalura a cikin yunwa mai tsanani, ba yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi An haramta muku mũshe da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da mãƙararriya da jefaffiya da mai gangarõwa da sõkakkiya, da abin da mãsu dãgi suka ci, fãce abin da kuka yanka, da abin da aka yanka a kan gunki (shĩ ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na cãca wannan fãsiƙanci ne, A yau waɗanda suka kãfirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Nã kammalã muku addininku, Kuma Nã cika ni'imaTa a kanku, Kuma Nã yarda da Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai tsanani, bã yana mai karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |