Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 31 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿فَبَعَثَ ٱللَّهُ غُرَابٗا يَبۡحَثُ فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيُرِيَهُۥ كَيۡفَ يُوَٰرِي سَوۡءَةَ أَخِيهِۚ قَالَ يَٰوَيۡلَتَىٰٓ أَعَجَزۡتُ أَنۡ أَكُونَ مِثۡلَ هَٰذَا ٱلۡغُرَابِ فَأُوَٰرِيَ سَوۡءَةَ أَخِيۖ فَأَصۡبَحَ مِنَ ٱلنَّٰدِمِينَ ﴾
[المَائدة: 31]
﴿فبعث الله غرابا يبحث في الأرض ليريه كيف يواري سوأة أخيه قال﴾ [المَائدة: 31]
Abubakar Mahmood Jummi Sai Allah Ya aiki wani hankaka, yana tono a cikin ƙasa domin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gawar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitona! Na kasa in kasance kamar wannan hankaka domin in turbuɗe gawar ɗan'uwana?" Sai ya wayi gari daga masu nadama |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai Allah Ya aiki wani hankaka, yana tono a cikin ƙasa domin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gawar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitona! Na kasa in kasance kamar wannan hankaka domin in turbuɗe gawar ɗan'uwana?" Sai ya wayi gari daga masu nadama |
Abubakar Mahmoud Gumi Sai Allah Ya aiki wani hankãka, yanã tõno a cikin ƙasa dõmin ya nuna masa yadda zai turbuɗe gãwar ɗan'uwansa. Ya ce: "Kaitõna! Nã kãsa in kasance kamar wannan hankãka dõmin in turbuɗe gãwar ɗan'uwana?" Sai ya wãyi gari daga mãsu nadãmã |