Quran with Hausa translation - Surah Al-Ma’idah ayat 64 - المَائدة - Page - Juz 6
﴿وَقَالَتِ ٱلۡيَهُودُ يَدُ ٱللَّهِ مَغۡلُولَةٌۚ غُلَّتۡ أَيۡدِيهِمۡ وَلُعِنُواْ بِمَا قَالُواْۘ بَلۡ يَدَاهُ مَبۡسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيۡفَ يَشَآءُۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرٗا مِّنۡهُم مَّآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ مِن رَّبِّكَ طُغۡيَٰنٗا وَكُفۡرٗاۚ وَأَلۡقَيۡنَا بَيۡنَهُمُ ٱلۡعَدَٰوَةَ وَٱلۡبَغۡضَآءَ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِۚ كُلَّمَآ أَوۡقَدُواْ نَارٗا لِّلۡحَرۡبِ أَطۡفَأَهَا ٱللَّهُۚ وَيَسۡعَوۡنَ فِي ٱلۡأَرۡضِ فَسَادٗاۚ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡمُفۡسِدِينَ ﴾
[المَائدة: 64]
﴿وقالت اليهود يد الله مغلولة غلت أيديهم ولعنوا بما قالوا بل يداه﴾ [المَائدة: 64]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne.* " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su saboda abin da suka faɗa. A'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yana ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yana ƙara wa masu yawa daga gare su, girman kai da kafirci. Kuma Mun jefa a tsakaninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Ranar ¡iyama, ko da yaushe suka hura wata wuta domin yaƙi, sai Allah Ya bice ta. Suna aiki a cikin ƙasa domin ɓarna, alhali kuwa Allah ba Ya son masu fasadi |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su saboda abin da suka faɗa. A'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yana ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yana ƙara wa masu yawa daga gare su, girman kai da kafirci. Kuma Mun jefa a tsakaninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Ranar ¡iyama, ko da yaushe suka hura wata wuta domin yaƙi, sai Allah Ya bice ta. Suna aiki a cikin ƙasa domin ɓarna, alhali kuwa Allah ba Ya son masu fasadi |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi |