Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 145 - الأنعَام - Page - Juz 8
﴿قُل لَّآ أَجِدُ فِي مَآ أُوحِيَ إِلَيَّ مُحَرَّمًا عَلَىٰ طَاعِمٖ يَطۡعَمُهُۥٓ إِلَّآ أَن يَكُونَ مَيۡتَةً أَوۡ دَمٗا مَّسۡفُوحًا أَوۡ لَحۡمَ خِنزِيرٖ فَإِنَّهُۥ رِجۡسٌ أَوۡ فِسۡقًا أُهِلَّ لِغَيۡرِ ٱللَّهِ بِهِۦۚ فَمَنِ ٱضۡطُرَّ غَيۡرَ بَاغٖ وَلَا عَادٖ فَإِنَّ رَبَّكَ غَفُورٞ رَّحِيمٞ ﴾
[الأنعَام: 145]
﴿قل لا أجد في ما أوحي إلي محرما على طاعم يطعمه إلا﴾ [الأنعَام: 145]
Abubakar Mahmood Jummi Ka ce: "Ba ni samu,* a cikin abin da aka yo wahayi zuwa gare Ni, abin haramtawa a kan wani mai ci wanda yake cin sa face idan ya kasance mushe ko kuwa jini abin zubarwa ko kuwa naman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, ko kuwa fasiƙanci wanda aka kururuta, domin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larura ta kama shi, ba mai fita jama'a ba, kuma ba mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Ba ni samu, a cikin abin da aka yo wahayi zuwa gare Ni, abin haramtawa a kan wani mai ci wanda yake cin sa face idan ya kasance mushe ko kuwa jini abin zubarwa ko kuwa naman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, ko kuwa fasiƙanci wanda aka kururuta, domin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larura ta kama shi, ba mai fita jama'a ba, kuma ba mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ka ce: "Bã ni sãmu, a cikin abin da aka yõ wahayi zuwa gare Ni, abin haramtãwa a kan wani mai ci wanda yake cin sa fãce idan ya kasance mũshe kõ kuwa jini abin zubarwa kõ kuwa nãman alade, to lalle ne shi ƙazanta ne, kõ kuwa fãsiƙanci wanda aka kurũrũta, dõmin wanin Allah da shi." Sa'an nan wanda larũra ta kãmã shi, bã mai fita jama'a ba, kuma bã mai ta'addi ba, to, lalle Ubangijinka Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |