Quran with Hausa translation - Surah Al-An‘am ayat 144 - الأنعَام - Page - Juz 8
﴿وَمِنَ ٱلۡإِبِلِ ٱثۡنَيۡنِ وَمِنَ ٱلۡبَقَرِ ٱثۡنَيۡنِۗ قُلۡ ءَآلذَّكَرَيۡنِ حَرَّمَ أَمِ ٱلۡأُنثَيَيۡنِ أَمَّا ٱشۡتَمَلَتۡ عَلَيۡهِ أَرۡحَامُ ٱلۡأُنثَيَيۡنِۖ أَمۡ كُنتُمۡ شُهَدَآءَ إِذۡ وَصَّىٰكُمُ ٱللَّهُ بِهَٰذَاۚ فَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّنِ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبٗا لِّيُضِلَّ ٱلنَّاسَ بِغَيۡرِ عِلۡمٍۚ إِنَّ ٱللَّهَ لَا يَهۡدِي ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ ﴾
[الأنعَام: 144]
﴿ومن الإبل اثنين ومن البقر اثنين قل آلذكرين حرم أم الأنثيين أما﴾ [الأنعَام: 144]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma daga raƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shanu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko matan biyu Ya hana, ko abin da mahaifar matan biyu suka tattara a kansa? Ko kun kasance halarce ne a lokacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, domin ya ɓatar da mutane ba da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah ba Ya shiryar da mutane Azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma daga raƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shanu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko matan biyu Ya hana, ko abin da mahaifar matan biyu suka tattara a kansa? Ko kun kasance halarce ne a lokacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, domin ya ɓatar da mutane ba da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma daga rãƙuma akwai nau'i biyu, kuma daga shãnu biyu; ka ce: Shin, mazan biyu ne Ya hana ko mãtan biyu Ya hana, kõ abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Kõ kun kasance halarce ne a lõkacin da Allah Ya yi muku wasiyya da wannan? To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, dõmin ya ɓatar da mutãne bã da wani ilmi ba? Lalle ne, Allah bã Ya shiryar da mutãne azzãlumai |