Quran with Hausa translation - Surah At-Taghabun ayat 14 - التغَابُن - Page - Juz 28
﴿يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِنَّ مِنۡ أَزۡوَٰجِكُمۡ وَأَوۡلَٰدِكُمۡ عَدُوّٗا لَّكُمۡ فَٱحۡذَرُوهُمۡۚ وَإِن تَعۡفُواْ وَتَصۡفَحُواْ وَتَغۡفِرُواْ فَإِنَّ ٱللَّهَ غَفُورٞ رَّحِيمٌ ﴾
[التغَابُن: 14]
﴿ياأيها الذين آمنوا إن من أزواجكم وأولادكم عدوا لكم فاحذروهم وإن تعفوا﴾ [التغَابُن: 14]
Abubakar Mahmood Jummi Ya ku waɗanda suka yi imani! Lalle ne daga matanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yafe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Ya ku waɗanda suka yi imani! Lalle ne daga matanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yafe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to, lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai |
Abubakar Mahmoud Gumi Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai |