Quran with Hausa translation - Surah Al-A‘raf ayat 143 - الأعرَاف - Page - Juz 9
﴿وَلَمَّا جَآءَ مُوسَىٰ لِمِيقَٰتِنَا وَكَلَّمَهُۥ رَبُّهُۥ قَالَ رَبِّ أَرِنِيٓ أَنظُرۡ إِلَيۡكَۚ قَالَ لَن تَرَىٰنِي وَلَٰكِنِ ٱنظُرۡ إِلَى ٱلۡجَبَلِ فَإِنِ ٱسۡتَقَرَّ مَكَانَهُۥ فَسَوۡفَ تَرَىٰنِيۚ فَلَمَّا تَجَلَّىٰ رَبُّهُۥ لِلۡجَبَلِ جَعَلَهُۥ دَكّٗا وَخَرَّ مُوسَىٰ صَعِقٗاۚ فَلَمَّآ أَفَاقَ قَالَ سُبۡحَٰنَكَ تُبۡتُ إِلَيۡكَ وَأَنَا۠ أَوَّلُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ﴾
[الأعرَاف: 143]
﴿ولما جاء موسى لميقاتنا وكلمه ربه قال رب أرني أنظر إليك قال﴾ [الأعرَاف: 143]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma a lokacin da Musa ya je ga mikatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Musa ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nuna mini in yi dubi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Ba za ka gan Ni ba, kuma amma ka duba zuwa ga dutse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, za ka gan Ni." Sa'an nan a lokacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dutsen, Ya sanya shi niƙaƙƙe. Kuma Musa ya faɗi somamme. To, a lokacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lokacin da Musa ya je ga mikatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Musa ya ce: "Ya Ubangijina! Ka nuna mini in yi dubi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Ba za ka gan Ni ba, kuma amma ka duba zuwa ga dutse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, za ka gan Ni." Sa'an nan a lokacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dutsen, Ya sanya shi niƙaƙƙe. Kuma Musa ya faɗi somamme. To, a lokacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Na tuba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma a lõkacin da Mũsã ya jẽ ga mĩkatinMu, kuma Ubangijinsa Ya yi masa magana, shi Mũsã ya ce: "Yã Ubangijina! Ka nũna mini in yi dũbi zuwa gare Ka!" Ya ce: "Bã zã ka gan Ni ba, kuma amma ka dũba zuwa ga dũtse, to, idan ya tabbata a wurinsa, to, zã ka gan Ni." Sa'an nan a lõkacin da Ubangijinsa, Ya kuranye zuwa ga dũtsen, Ya sanyã shi niƙaƙƙe. Kuma Mũsã ya fãɗi sõmamme. To, a lõkacin da ya farka, ya ce: "TsarkinKa ya tabbata! Nã tũba zuwa gare Ka, kuma ni ne farkon mũminai |