Quran with Hausa translation - Surah Al-A‘raf ayat 85 - الأعرَاف - Page - Juz 8
﴿وَإِلَىٰ مَدۡيَنَ أَخَاهُمۡ شُعَيۡبٗاۚ قَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥۖ قَدۡ جَآءَتۡكُم بَيِّنَةٞ مِّن رَّبِّكُمۡۖ فَأَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَٱلۡمِيزَانَ وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تُفۡسِدُواْ فِي ٱلۡأَرۡضِ بَعۡدَ إِصۡلَٰحِهَاۚ ذَٰلِكُمۡ خَيۡرٞ لَّكُمۡ إِن كُنتُم مُّؤۡمِنِينَ ﴾
[الأعرَاف: 85]
﴿وإلى مدين أخاهم شعيبا قال ياقوم اعبدوا الله ما لكم من إله﴾ [الأعرَاف: 85]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah; ba ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku ta zo muku! Sai ku cika mudu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutane kayansu, kuma kada ku yi fasadi a cikin ƙasa a bayan gyaranta. Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah; ba ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku ta zo muku! Sai ku cika mudu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutane kayansu, kuma kada ku yi fasadi a cikin ƙasa a bayan gyaranta. Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance muminai |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma zuwa Madayana ɗan'uwansu Shu'aibu, ya ce: "Ya mutãnena! Ku bauta wa Allah; bã ku da wani abin bauta wa waninSa. Lalle ne, wata hujja bayyananniya daga Ubangijinku tã zõ muku! Sai ku cika mũdu da sikeli kumakada ku nakasa wa mutãne kãyansu, kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa a bãyan gyaranta. Wannan ne mafi alhẽri a gare ku, idan kun kasance mũminai |