| وَالْمُرْسَلَاتِ عُرْفًا (1) Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna
 | 
| فَالْعَاصِفَاتِ عَصْفًا (2) Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi
 | 
| وَالنَّاشِرَاتِ نَشْرًا (3) Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa
 | 
| فَالْفَارِقَاتِ فَرْقًا (4) sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa
 | 
| فَالْمُلْقِيَاتِ ذِكْرًا (5) Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni
 | 
| عُذْرًا أَوْ نُذْرًا (6) Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi
 | 
| إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَاقِعٌ (7) Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne
 | 
| فَإِذَا النُّجُومُ طُمِسَتْ (8) To, idan taurãri aka shãfe haskensu
 | 
| وَإِذَا السَّمَاءُ فُرِجَتْ (9) Kuma, idan sama aka tsãge ta
 | 
| وَإِذَا الْجِبَالُ نُسِفَتْ (10) Kuma, idan duwãtsu aka nike su
 | 
| وَإِذَا الرُّسُلُ أُقِّتَتْ (11) Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su
 | 
| لِأَيِّ يَوْمٍ أُجِّلَتْ (12) Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali
 | 
| لِيَوْمِ الْفَصْلِ (13) Domin rãnar rarrabẽwa
 | 
| وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الْفَصْلِ (14) Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (15) Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| أَلَمْ نُهْلِكِ الْأَوَّلِينَ (16) Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba
 | 
| ثُمَّ نُتْبِعُهُمُ الْآخِرِينَ (17) Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe
 | 
| كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ (18) Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (19) Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| أَلَمْ نَخْلُقكُّم مِّن مَّاءٍ مَّهِينٍ (20) Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba
 | 
| فَجَعَلْنَاهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ (21) Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce
 | 
| إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعْلُومٍ (22) Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna
 | 
| فَقَدَرْنَا فَنِعْمَ الْقَادِرُونَ (23) Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (24) Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ كِفَاتًا (25) Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba
 | 
| أَحْيَاءً وَأَمْوَاتًا (26) Ga rãyayyu da matattu
 | 
| وَجَعَلْنَا فِيهَا رَوَاسِيَ شَامِخَاتٍ وَأَسْقَيْنَاكُم مَّاءً فُرَاتًا (27) Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (28) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| انطَلِقُوا إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِ تُكَذِّبُونَ (29) Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi
 | 
| انطَلِقُوا إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَاثِ شُعَبٍ (30) Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku
 | 
| لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغْنِي مِنَ اللَّهَبِ (31) Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta
 | 
| إِنَّهَا تَرْمِي بِشَرَرٍ كَالْقَصْرِ (32) Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye
 | 
| كَأَنَّهُ جِمَالَتٌ صُفْرٌ (33) Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (34) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| هَٰذَا يَوْمُ لَا يَنطِقُونَ (35) Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba
 | 
| وَلَا يُؤْذَنُ لَهُمْ فَيَعْتَذِرُونَ (36) Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (37) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| هَٰذَا يَوْمُ الْفَصْلِ ۖ جَمَعْنَاكُمْ وَالْأَوَّلِينَ (38) Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko
 | 
| فَإِن كَانَ لَكُمْ كَيْدٌ فَكِيدُونِ (39) To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (40) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي ظِلَالٍ وَعُيُونٍ (41) Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari
 | 
| وَفَوَاكِهَ مِمَّا يَشْتَهُونَ (42) Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari
 | 
| كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (43) (A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa
 | 
| إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجْزِي الْمُحْسِنِينَ (44) Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (45) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| كُلُوا وَتَمَتَّعُوا قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجْرِمُونَ (46) (Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (47) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ارْكَعُوا لَا يَرْكَعُونَ (48) Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba
 | 
| وَيْلٌ يَوْمَئِذٍ لِّلْمُكَذِّبِينَ (49) Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa
 | 
| فَبِأَيِّ حَدِيثٍ بَعْدَهُ يُؤْمِنُونَ (50) To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni
 |