Quran with Hausa translation - Surah Yunus ayat 71 - يُونس - Page - Juz 11
﴿۞ وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ نُوحٍ إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦ يَٰقَوۡمِ إِن كَانَ كَبُرَ عَلَيۡكُم مَّقَامِي وَتَذۡكِيرِي بِـَٔايَٰتِ ٱللَّهِ فَعَلَى ٱللَّهِ تَوَكَّلۡتُ فَأَجۡمِعُوٓاْ أَمۡرَكُمۡ وَشُرَكَآءَكُمۡ ثُمَّ لَا يَكُنۡ أَمۡرُكُمۡ عَلَيۡكُمۡ غُمَّةٗ ثُمَّ ٱقۡضُوٓاْ إِلَيَّ وَلَا تُنظِرُونِ ﴾
[يُونس: 71]
﴿واتل عليهم نبأ نوح إذ قال لقومه ياقوم إن كان كبر عليكم﴾ [يُونس: 71]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma ka karanta musu labarin Nuhu, a lokacin da ya ce wa mutanensa, "Ya mutanena! Idan matsayina da tunatarwata ameda ayoyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dogara. Sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka karanta musu labarin Nuhu, a lokacin da ya ce wa mutanensa, "Ya mutanena! Idan matsayina da tunatarwata ameda ayoyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dogara. Sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka karanta musu lãbãrin Nũhu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa, "Ya mutãnẽna! Idan matsayĩna da tunãtarwata ameda ãyõyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dõgara. Sai ku tãra al'amarinku, kũ da abũbuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri |