Quran with Hausa translation - Surah Al-Kahf ayat 29 - الكَهف - Page - Juz 15
﴿وَقُلِ ٱلۡحَقُّ مِن رَّبِّكُمۡۖ فَمَن شَآءَ فَلۡيُؤۡمِن وَمَن شَآءَ فَلۡيَكۡفُرۡۚ إِنَّآ أَعۡتَدۡنَا لِلظَّٰلِمِينَ نَارًا أَحَاطَ بِهِمۡ سُرَادِقُهَاۚ وَإِن يَسۡتَغِيثُواْ يُغَاثُواْ بِمَآءٖ كَٱلۡمُهۡلِ يَشۡوِي ٱلۡوُجُوهَۚ بِئۡسَ ٱلشَّرَابُ وَسَآءَتۡ مُرۡتَفَقًا ﴾
[الكَهف: 29]
﴿وقل الحق من ربكم فمن شاء فليؤمن ومن شاء فليكفر إنا أعتدنا﴾ [الكَهف: 29]
Abubakar Mahmood Jummi Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Saboda haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Lalle ne Mu, Mun yi tattali domin azzalumai wata wuta wadda shamakunta, sun ƙewaye da su. Kuma idan sun nemi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yana soye fuskoki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi munin zama mahutarsu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Saboda haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Lalle ne Mu, Mun yi tattali domin azzalumai wata wuta wadda shamakunta, sun ƙewaye da su. Kuma idan sun nemi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yana soye fuskoki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi munin zama mahutarsu |
Abubakar Mahmoud Gumi Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Sabõda haka wanda ya so, to, ya yi ĩmãni, kuma wanda ya so, to, ya kãfirta. Lalle ne Mũ, Mun yi tattali dõmin azzãlumai wata wuta wadda shãmakunta, sun ƙẽwaye da su. Kuma idan sun nẽmi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yanã sõye fuskõki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi mũnin zama mahũtarsu |