Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 140 - البَقَرَة - Page - Juz 1
﴿أَمۡ تَقُولُونَ إِنَّ إِبۡرَٰهِـۧمَ وَإِسۡمَٰعِيلَ وَإِسۡحَٰقَ وَيَعۡقُوبَ وَٱلۡأَسۡبَاطَ كَانُواْ هُودًا أَوۡ نَصَٰرَىٰۗ قُلۡ ءَأَنتُمۡ أَعۡلَمُ أَمِ ٱللَّهُۗ وَمَنۡ أَظۡلَمُ مِمَّن كَتَمَ شَهَٰدَةً عِندَهُۥ مِنَ ٱللَّهِۗ وَمَا ٱللَّهُ بِغَٰفِلٍ عَمَّا تَعۡمَلُونَ ﴾
[البَقَرَة: 140]
﴿أم تقولون إن إبراهيم وإسماعيل وإسحاق ويعقوب والأسباط كانوا هودا أو نصارى﴾ [البَقَرَة: 140]
Abubakar Mahmood Jummi Ko kuna cewa: Lalle ne, Ibrahim da Isma'ila da Is'haƙa da Ya'aƙubu da Jikoki, sun kasance Yahudawa ko kuwa Nasara? Ka ce: Shin ku ne kuke mafi sani koAllah? Kuma wane ne ya zama mafi zalunci daga wanda ya boye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Ko kuna cewa: Lalle ne, Ibrahim da Isma'ila da Is'haƙa da Ya'aƙubu da Jikoki, sun kasance Yahudawa ko kuwa Nasara? Ka ce: Shin ku ne kuke mafi sani koAllah? Kuma wane ne ya zama mafi zalunci daga wanda ya boye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatawa |
Abubakar Mahmoud Gumi Ko kuna cẽwa: Lalle ne, Ibrãhĩm da Ismã'ĩla da Is'hãƙa da Ya'aƙũbu da Jĩkõki, sun kasance Yahũdãwa kõ kuwa Nasãra? Ka ce: Shin kũ ne kuke mafi sani kõAllah? Kuma wãne ne ya zama mafi zãlunci daga wanda ya bõye shaida a wurinsa daga Allah? Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga abin da kuke aikatãwa |