Quran with Hausa translation - Surah Al-Baqarah ayat 197 - البَقَرَة - Page - Juz 2
﴿ٱلۡحَجُّ أَشۡهُرٞ مَّعۡلُومَٰتٞۚ فَمَن فَرَضَ فِيهِنَّ ٱلۡحَجَّ فَلَا رَفَثَ وَلَا فُسُوقَ وَلَا جِدَالَ فِي ٱلۡحَجِّۗ وَمَا تَفۡعَلُواْ مِنۡ خَيۡرٖ يَعۡلَمۡهُ ٱللَّهُۗ وَتَزَوَّدُواْ فَإِنَّ خَيۡرَ ٱلزَّادِ ٱلتَّقۡوَىٰۖ وَٱتَّقُونِ يَٰٓأُوْلِي ٱلۡأَلۡبَٰبِ ﴾
[البَقَرَة: 197]
﴿الحج أشهر معلومات فمن فرض فيهن الحج فلا رفث ولا فسوق ولا﴾ [البَقَرَة: 197]
Abubakar Mahmood Jummi Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji* a cikinsu to babu jima'i kuma babu fasiƙanci, kuma babu jayayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alherin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula |
Abubakar Mahmoud Gumi Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to babu jima'i kuma babu fasiƙanci, kuma babu jayayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alherin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula |
Abubakar Mahmoud Gumi Hajji watanni ne sanannu. To, wanda ya yi niyyar hajji a cikinsu to bãbu jimã'i kuma bãbu fãsiƙanci, kuma bãbu jãyayya a cikin hajji. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, Allah Ya san shi. Kuma ku yi guzuri. To, mafi alhẽrin guzuri yin taƙawa. Kuma ku bi Ni da taƙawa, ya ma'abuta hankula |